Gabanin gangamin siyasar da za a yi a jihar Akwa Ibom, Buhari ya ba Akpabio muƙami

199

Gabanin ƙaddamar da gangamin yaƙin sake neman zaɓen Shugaba Muhammadu Buhari a yankin Kudu Maso Kudu da za a yi gobe Juma’a a jihar Akwa Ibom, Shugaba Muhammadu Buhari ya naɗa Sanata Godswill Akpabio a matsayin Shugaban Kwamitin Tallafawa Takarar Shugaban Ƙasa na Ƙasa.

Fasto Mpon Okon, Shugaban Kwamitin na Jihar Akwa Ibom wanda ya bayyana haka ranar Alhamis ya ce Shugaban kuma ya naɗa ‘yan asalin jihar su huɗu zuwa cikin Kwamitin.

Waɗanda aka naɗa ɗin sun haɗa da Lady Valerie Ebe, wadda tsohuwar Mataimakiyar Gwamnan Jihar ce a matsayin Shugabar Kwamitin Bada Shawara, Sanata John Akpanudoedehe a matsayin Daraktan Tsare-tsare da Dabaru na Ƙasa, Sanata Aloysius Etok a matsayin Daraktan Kula da Dangantaka Tsakanin Jam’iyyu na Ƙasa, da Shugabar Matar Jam’iyyar APC a yankin Kudu Maso Kudun, Misis Rachael Akpabio a matsayin Mataimakiyar Sakataren Walwala.

Mista Okon ya ce naɗe-naɗen sun nuna irin ƙwarin gwiwar da Shugaba Buhari yake da shi game da su, da damar da suke da ita na yin aiki cikin nasara domin tabbatar da nasararsa a zaɓe mai zuwa.

Ya yi kira ga al’ummar jihar ta Akwa Ibom da su shiga al’amuran siyasar ƙasa gadan-gadan ta hanyar goya wa jam’iyyar APC baya ta dawo ta ci zaɓen Shugaban Ƙasa, su kuma tabbatar da cewa jam’iyyar ta lashe zaɓen jihar a shekara t a 2019.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan