UTME 2019: JAMB za ta fara yi wa ɗalibai rijista ranar 10 ga Janairun 2019

291

Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Makarantun Gaba da Sakandare, JAMB ta ce za ta fara rijistar Jarrabawar Bai Ɗaya ta Shiga Manyan Makarantu, UTME ta shekara ta 2019 ranar 10 ga watan Janairun 2019.

Magatakardar JAMB ɗin, Farfesa Ishaq Oloyede ya faɗa a wani taron ganawa na masu ruwa da tsakin masu Cibiyoyin Ɗaukar Jarrabawar da ake yi wa laƙabi da CBT Centres da kuma saura a Jami’ar Jihar Legas ranar Alhamis cewa siyar da katin yin rijista na e-PINS mai amfani da fasahar Intanet zai ɗauki tsawon makonni shida, amma bai sanar da haƙiƙanin ranakun da za a yi jarrabawar ba.

Tun da farko dai Mista Oloyede ya sanar da ranar 3 ga watan Janairu a matsayin ranar da za a fara siyar da fama-famai, amma ya canza ranar zuwa 10 ga watan Janairun 2019 biyo bayan roƙo da masu Cibiyoyin Ɗaukar Jarrabawar suka yi na ƙarin lokaci don su samu damar kammala gwajin rumbun adana bayanansu na Intanet.

An ba cibiyoyin wa’adin kwana bakwai daga yau don kammala gwajin da zai tabbatar da cewa kwamfiyoticin nasu suna cikin shiri, za kuma su iya saduwa da Babban Ɗakin Sadarwa na JAMB dake Abuja. Amma an ƙara tsawon kwanakin bayan da masu Cibiyoyin Ɗaukar Jarrabawar suka yi roƙon ƙarin lokaci.

Mista Oloyede ya ce Cibiyoyin Ɗaukar Jarrabawar guda 718 da aka amince da su a faɗin ƙasar nan su kaɗai ne za su yi wa ɗalibai rijistar.

Ya ce an shigo da abubuwa da dama don a tabbatar da cewa masu ɗaukar jarrabawar suna da iko sosai da bayanansu da suka ba Hukumar lokacin yin rijistar.

Magatakardar JAMB ɗin ya gode wa Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC sakamako aiki da Hukumar tare wajen shirya jadawalin zaɓe.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan