Home / Gwamnati / Ka mika kanka ga ‘yan sanda- Shehu Sani ya shawarci Dino Melaye

Ka mika kanka ga ‘yan sanda- Shehu Sani ya shawarci Dino Melaye

Sanata Mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya shawarci takwaransa dake wakiltar Kogi ta Yamma, Dino Melaye, da ya mika kansa da kansa ga ‘yan sanda.

Za a iya tunawa cewa jami’an ‘yan sanda sun je gidan Mista Melaye don kama shi bisa zargin harbin wani sajan da dan sanda, Danjuma Saliu dake aiki da Rundunar ‘Yan Sanda ta 37, PMB yayin da yake bakin aiki a Aiyetoro Gbede a kan Titin Mopa a jihar Kogi.

Mista Sani ya bada shawarar ne biyo bayan wasan buyar da ake yi tsakanin Rundunar ‘Yan Sanda ta Kasa da dan siyasar haifaffen jihar Kogi.

Da yake bada shawarar a shafinsa na Twitter, Mista Sani ya ce: ” Ya kamata jami’an ‘yan sanda su kawo karshen mamayar da suke yi wa gidan Sanata Dino Melaye, shi ma Sanata ya kamata ya mika kansa da kansa ga ‘yan sanda tare da lauyoyinsa.

“Wannan mamaye irin na Gaza ba zai taimaki kumar Rundunar ‘Yan Sanda ta Kasa, gwamnati da kasa ba”.

Amma Daily Nigerian ta gano cewa jami’an ‘yan sanda sun ci gaba da yin tsinke a gidan Sanatan dan jam’iyyar PDP har tsawon awa 48.

Rundunar ‘Yan Sandan, a sanarwarta ta ce jami’an nata da aka tura don kamo Mista Melaye a gidansa ba za su sassauta ba har sai Sanatan ya mika kansa don a kama shi a kuma bincike shi.

About Labarai24

Wannan Jarida ce ta shafin Intanet dake kawo muku labarai da rahotannin. har da Bidiyo da Audio.

Check Also

Shugabannin Addini Da Na Siyasa Na Ƙoƙarin Kifar Da Gwamnatina— Buhari

Fadar Shugaban Najeriya ta ce wasu ‘yan Najeriya marasa kishin ƙasa na ƙoƙarin haɗa kai …

One comment

  1. Do you have any ideas for creating short articles?
    That’s where I constantly struggle and I simply wind up looking vacant display for lengthy time.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *