Tambuwal ya bada hutu don yi wa Shagari addu’a

163

Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana ranar Litinin, 31 ga watan Disamban 2018 a matsayin ranar hutu a jihar don ba mazauna jihar dama yin addu’o’i na musamman domin neman Allah Ya gafarta wa tsohon shugaban ƙasa, Alhaji Shehu Usmanu Aliyu Shagari.

 

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan Janar na Wata Labarai da Huɗɗa da Jama’a na gwamnan, Abubakar Shekara ya fitar kuma aka raba wa manema labarai a Sakkwato ranar Asabar.
Gwamna Tambuwal ya ce bada sanarwar ya biyo bayan tuntuɓar Majalisar Sarkin Musulmi.


“Sakamakon haka gwamnatin jihar ta buƙaci limamai da al’umma gaba ɗaya a dukkan faɗin jihar da su sadaukar da ranar wajen yin addu’o’i na musamman don neman rahama ga ruhin tsohon shugaban ƙasa da samun zaman lafiya da ci gaban ƙasa gaba ɗaya.
“Gwamnatin ta umarci da a sauko da tutoci ƙasa-ƙasa a harabobin cibiyoyin gwamnati da masu zaman kansu don girmama marigayi tsohon shugaban ƙasar, Shehu Shagari”, in ji sanarwar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan