Ba mu cimma wata yarjejeniya da gwamnati ba- ASUU

141

A ranar Larabar nan ne Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa, ASUU ta karyata ikirarin Gwamnatin Tarayya cewa sun cimma yarjejeniya da kungiyar game da yajin aikin da ta dauki tsawon wata biyu tana yi.

Shugaban ASUU na Kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi shi ne ya bayyana haka lokacin wata ganawa ta musamman da jaridar TribuneOnline.

A cewarsa, har yanzu tattaunawa
tsakanin Gwamnatin Tarayya da ASUU ba ta kammala ba saboda bangaren da ya wakilci ASUU a lokacin ganawarsu da gwamnati ba shi yake da maganar karshe ba game da janye yajin aikin.

Ya bayyana cewa abinda su ke da shi a kasa a halin yanzu daga gwamnati shi ne tayi, wanda ASUU ta nace cewa dole a rubuta, a kuma nuna yadda za a tsara cika alkawura, ba kamar yadda gwamnati ta saba yi musu alkawarin baki ba tun da aka fara yajin aikin tsawon watanni biyu.

Ganawarsu ta karshe ita ce ta bakwai tunda ASUU ta fara yajin aikin, amma har yanzu ba a cimma takamaimiyar matsaya ba.

Farfesa Ogunyemi ya ce jiya Talata ne gwamnati ta aika musu da tayin, ba kuma tare da ta tsaya ta saurari ta bakinsu ba ta tafi bainar jama’a tana cewa ta cimma yarjejeniya da ASUU. Farfesan ya ce ba haka ASUU take aiki ba.

Ya bayyana cewa wakilan da su ka wakilci ASUU a wajen ganawar dole su tuntubi shugabancin ASUU kafin yanke hukunci na gaba.

Farfesa Ogunyemi ya kara da cewa Babban Kwamitin Zartarwar ASUU shi kadai ya ke da maganar karshe game da kowane irin hukunci.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan