Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince cewa ana samun koma-baya a fafutukar kakkabe mayakan Boko Haram musamman a yankin arewa maso gabashin kasar.
A yayin wata hirarsa da aka watsa ta kafar talabijin ta Arise, shugaba Buhari ya amince cewa, sojojin kasar na fuskantar matsin lamba daga mayakan na Boko Haram da ke amfani da salon yakin sunkuru.
Shugaban ya kuma amince cewa, sojojin kasar na fama da matsalar rashin karfafa musu guiwa a fagen-daga, amma ya ce, suna kan kokarin shawo kan wannan matsalar.
“ Akwai abin da zan kira gajiyawar yaki” in jin Buhari wanda ya kara da cewa, sake bai wa sojojin horo zai magance dabarun mayakan masu ikirarin jihadi.
Sojojin da ke fagen-daga sun sha korafi kan cewa, mayakan na Boko Haram sun mallaki makaman da suka zarce nasu, kuma ba sa samun kwarin guiwa yadda ya kamata a cewarsu.
A bangare guda, shugaban ya ce, yana nazari akan korafin rashin sallamar manyan hafsoshin tsaronsa bayan tsanantar hare-haren Boko Haram a baya-bayan nan.