Tirƙashi: Gabannin zaɓen 2019 Ministar Buhari ta bar aiki

110

Karamar Ministar Harkokin Kasashen Waje, Khadija Ibrahim ta ajiye mukaminta don yin takarar Majalisar Wakilai a zaben 16 ga watan Fabrairu.
Misis Ibrahim ta tabbatar wa da wasu ‘yan jaridun Fadar Gwamnati cewa Taron Ganawar Majalisar Zartarwa ta Kasa na yau Laraba shi ne na karshe da za ta halarta.
Ta yi jawabi a takaice kafin a fara taron ganawar.
Barin aikin nata na zuwa wata daya bayan tsohon Karamin Ministan Muhalli, Ibrahim Jubril ya bar aiki sakamakon zaben sa da aka yi a matsayin Sarkin Nasarawa na 13.
Misis Ibrahim tana takarar wakiltar Mazabar dan Majalisar Tarayya ta Damaturu/Tarmuwa/Gujba/Gulani.
Ta kayar da Mohammed Ibrahim a zaben fitar da gwani da aka yi, abinda ya ba ta damar zama ‘yar takarar jam’iyyar APC.
Ta samu kuri’a 1,295 yayinda abokin karawar tata ya samu kuri’a 15.
Shugaba Muhammadu Buha ya nada Misis Ibrahim ne a matsayin minista a shekara ta 2015.
A lokacin zaben Majalisar Dokoki na shekara ta 2015, an zabe ta don ta wakilci Damaturu/Tarmuwa/Gujba/Gulani.
Bayan ta kama aiki a Majalisar Dokokin ne nan sai Shugaba Muhammadu Buhari ya nada ta minista.
Misis Ibrahim, ‘yar shekara 52, matar tsohon Gwamnan Jihar Yobe ce, Bukar Abba Ibrahim, wanda ya yi gwamnan jihar Yoben har sau uku, kuma sanata ne mai ci a halin yanzu. Tsohon gwamnan ba ya neman a sake zaben sa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan