Kisan kiyashin jihar Zamfara: Al’umomi na kokawa yayinda su ke zargin ‘yan siyasa, jami’an tsaro da sarakunan gargajiya da hannu (1)

1113

Kisan kiyashin da ke ci gaba da afkuwa a halin yanzu a jihar Zamfara wanda aka gagara shawo kansa ya ci gaba da afkuwa ne sakamakon irin alfanun da ‘yan siyasa, jami’an tsaro da sarakunan gargajiya ke samu daga kashe-kashen, jaridar WikkiTimes ta yi rahoton dake tabbatar da haka.

Mazauna kauyukan da hare-haren su ka shafa kai tsaye, ‘yan kato da gora da kungiyoyin fararen hula na zargin sarakunan gargajiya, wasu jami’an ‘yan sanda da kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar akan harkokin tsaro da taimakon hare-haren.

Haruna Muhammed Salisu, wanda ya ziyarci hudu daga cikin kananan hukumomin da abin ya fi shafa a yankunan mazabar sanata guda uku ya yi rahoto game da yadda mahara ke ci gaba da kai wa alu’momi hare-hare ba tare da samun wani tallafi ba.

Da misalin karfe 6:30 na safe, lokacin ake cikin yanayin hazo, iska da sanyi, mata da yara masu mabanbantan shekaru, wadanda suke rawar sanyi tare da hade hakora, wadanda kuma suke daga makobtan kauyuka suka fara shiga garin Nasarawan Godal dake karamar hukumar Birnin Magaji.

Mutanen da adadinsu ya kusa 200, matan da kananan yaran suna barin garin ne gungu-gungu daga kauyukan Garin Kaka, Garin Haladu da Garin Dandambo wadanda duka nisansu bai wuce kilomita 10 ba daga Nasarawan Godal, gari na biyu mafi girma a karamar hukumar Birnin Magaji.

Mahara da su ka addadbi dukkan kananan hukumomi 14 na jihar Zamfara tun shekarar 2011 sun kai wa wadannan kauyuka hari a daren da ya gabata.
Abu mai tayar da hankali game da wadannan mata da kananan yara shi ne dawowarsu Nasarawan Godal ranar 26 ga watan Disamba, 2018 ita ce ta biyu a cikin mako daya, kuma ta goma a cikin makonni shida.

Wannan mai daukar rahoto zai iya ganin rudewa, tsoro da damuwa a fuskokinsu saboda da yawan su su na kukan yunwa. Ana iya ganin ‘ya’yansu suna kuka, suna rokon abinci da ruwa daga iyayensu mata, amma abin kaico iyayen nasu mata ba za su iya taimakon su ba.

Wannan mai daukar rahoto ya siyo abinci ya raba wa wadannan mata masu barin garuruwansu.
Ko dai an kashe kananan ‘ya’yansu maza ko kuma sun gudu zuwa cikin daji don tsira.
A ranar harin Kirsimeti, maharan sun kashe mutum 23 (dukkanin su maza manya) a kauyuka hudun da suka yi wa kawanya.

Yayinda wasu daga cikin masu dawowa garin ke yawo ba takalmi, suna jan kannensu da wasu daga cikin dabbobinsu, wasu kuwa sun yi amfani ne da amalanke don dauko kannensu da wasu ‘yan kayayyakinsu da za su iya dauka.

A cikin wadanda suka dawo din akwai Hauwa, ‘yar shekara 38, wadda aka shirya bikin sunan danta ranar Alhamis, 27 ga watan Disamba, 2018, amma tilas ta bar kauyen nasu ta tafi Nasarawan Godal duk da kammala dukkan shirye-shiryen da suka wajaba na bikin sunan.

Kusan Hauwa ta tsira daga harin ranar Kirsimetin ba tare da wani abu ba face tufafin da take sanye da shi, da kuma zanin goyon da ta ke amfani da shi don goya jaririn.

Abin takaici, mahaifiyar ba ta iya dauko wa jaririn mai kwana biyar wani tufafi ba, balle kuma rigar sanyin da za ta kare ta daga muku-mukun sanyi da aka yi a wannan rana.

Lokacin da ta sauka Nasarawan Godal, Hauwa da sauran abokan tafiyarta da suka dawo garin tare suka tafi gidajen dangi inda suka fake kafin su koma kauyukansu.

Wannan tafiya ta a je a dawo kusan ta zama jiki tsakanin wadannan mazauna karkara da kuma al’umomin da suke karbarsu, saboda a halin yanzu ba wani sansani da zai iya karbar su duk da maimaituwar haren-haren.

A dukkan kananan hukumomi 14 na jihar Zamfara, kauyuka sun kasance karkashin hare-haren mahara dauke da makamai, wadanda sun kashe fiye da mutane 3,000 sun kuma lalata kauyuka babu adadi.

Wuraren da abin ya fi muni su ne kananan hukumomin Birnin Magaji, Maradun, Zurmi da Tsafe, inda kashe-kashe, sace mutane, neman kudin fansa, kona kauyuka, satar shanu da lalata gonaki ya zama ruwan dare.

Wadanda abin ya shafa suna kuka da biyan kudin fansa da kashe musu masoya

Maharan dauke da makamai idan su ka kai hari su kan yi kisa yadda su ka ga dama, su yi wa matan da ba su ji ba ba su gani ba fyade, su lalata dukiya, su kuma sace mutane don neman kudin fansa.

Misali, Sani Magaji (an boye ainihin sunansa saboda dalilan tsaro) an sace masa ‘ya’yansa maza, dan shekara 15 da dan shekara 13 a cikin wata daya a shekara ta 2018.

A hari na biyu, maharan su kashe daya daga cikin dattawan gidan a kokarinsu na bijirewa sakamakon rasa kudi masu dimbin yawa wajen biyan kudin fansa a harin baya.

A cewar Magaji, maharan sun farma kauyen nasu ne suka fara harbin kan mai uwa da wabi. Ana cikin rudewa, mutane su ka fara gudu ba ji ba gani don gudun ko dai kar maharan su kashe su ko su sace su. Dansa Abubakar, bai yi sa’a ya tsira tare da sauran iyalan gidan ba, ya fada hannun maharan.

Don a samu a sake shi, Magaji ya ce sai da iyalan su ka tattara Miliyan 1.7 a matsayin kudin fansa, sun tattara kudin ne ta hanyar siyar da filaye da su ka hada da gonaki.

Makonni shida bayan haka, maharan su ka dawo gidan su Magaji, inda su ka sace wani babban mai fada a ji a gidan, kuma su ka sace yaro na biyu, wanda su ka tattara Miliyan 1.3 a don biyan kudin fansarsa.

A wannan lokaci, iyalan, a cewar Magaji ba su iya hada kudin da aka bukata ba kafin cikar wa’adin, saboda ba wanda ya siyi gonar da su ka daga don siyarwa a garin.

Lokacin da wa’adin ya kare, maharan su ka kashe yaron dan shekara 13 duk da rokon da aka yi ta musu na su kara wa’adin biyan kudin fansar.

A wani wajen kuma a karamar hukumar Tsafe, matar Malam Adamu Asaula ta yi kwana uku a hannun masu garkuwa da mutane, inda su ka yi mata fyade babu adadi kafin ta samu ‘yanci.

Ta gamu da wannan ibtila’i ne lokacin da maharan su ka kai hari kauyensu, su ka kuma dauke ta da karfi. Amma ba su bukaci kudin fansa ba, sai su ka ce su na so su mayar da ita matarsu.

Ta samu sa’ar tsira ne lokacin da ‘yan kato da gora su ka dira a maboyar maharan, inda su ka gudu su ka bar ta a cikin radadi.

A halin yanzu matar da aka sace din da sauran ‘yan gidan su na zaune a Makarantar ‘Yan Mata ta Gwamnati dake Tsafe, GGDSS, Tsafe.

Maharan su kai wa kauyensu na Asaula hari, kuma a halin yanzu mazauna kauyen su na tsoron komawa, saboda ba zai zaunu ba.

Banda garkuwa da mutane, kashe-kashe, lalata dukiya, maharan su kan sace shanu da duk wani abu da su ka ga yana da kima idan su ka kai hari.

A kauyen Tsabre dake karamar hukumar Birnin Magaji, maharan sun sace fiye da shanu 200 a watan Oktoban 2018, da awakai da tumakai da su ka kai 400 a hari daya kawai.

Wadanda harbin bindiga ya shafa

Da a ce maharan sun yi nasara,da
Sanusi Bawa, wani yaro dan shekara 17 ya zama wanda ba zai iya haihuwa ba.

A ranar Kirsimeti, maharan dauke da makamai su ka kai wa Sanusi hari, dan uwansa Garba da mahaifinsu yayin da su ke aiki a gonarsu ta dankali dake Garin Kaka.

Maharan sun kashe dan uwan Sanusi, Garba, mai shekara 14. Mahaifinsu Malam Bawa ya tsira ba tare da sun yi masa komai ba.

A halin yanzu, Sanusi ya na samun kulawa sakamakon harbin bindiga a al’aurarsa a Amfani Medical Centre (wani asibiti mai zaman kansa) da ke Nasarawan Godal.
Harsashin bindigar ne ya wuce ta kan al’aurarsa.

Ba Sanusi kadai ne yake samun kulawa sakamakon makamancin irin wannan hari a wannan asibitin ba.

Shehu, dan shekara 42 da ke da ‘ya’ya 16 da mata uku shi ma ya na jiyya a asibitin sakamakon harbin bindiga a cikinsa.

Maharan dai su ka kai kari a kauyensu na Garin Haladu a dai harin ranar Kirsimetin da ya hada da kauyuka uku.

Kamar yadda ya faru da Sanusi, harsashi ne ya shiga saman cikin Shehu ta bangaren dama.

Da harsashin ya shiga cikin Shehu, da ya lalata masa manyan sassan jikinsa, kamar hanta, da tuni kuwa ya ce ga garinku nan.

Akwai Umar, dan shekara 22, wanda ya samu harbin harsashi a cinyarsa ta hagu, shi ma yana jiyya a Amfani Medical Centre din.

Za a iya bayyana Shehu, Sanusi da Umar a matsayin wadanda su ka fi kowa sa’a ranar da maharan su ka kai hari a kauyukansu. A wannan rana, maharan su kashe mutane 23.

A watan Nuwamban 2018, an dauki mutane hudu zuwa asibiti a Gusau sakamakon harbin da su ka samu a harin da aka kai kauyen Gidan Geru dake yankin karamar hukumar Maradun. Kauyukan Gidan Geru, Falau, Magami da Ruwan Bado su ma sun samu hare-haren maharan, inda su ka kashe mutane 18.

A dukkan haren-haren nan, wadanda abin ya shafa su ne su ke daukar nauyin kudaden magani yawanci kuma a asibitoci masu zaman kansu, sakamakon rashin kayan aiki, magani da rashin ma’aikata a garuruwan dake kusa da su.

Babu ayyukan jin kai a wadannan kauyuka

Wannan rikici na Zamfara ya haifar da wahalhalu a rayuwar jama’a a kauyuka daban-daban, ya tsayar da harkokin tattalin arziki, ya dakatar da karatun yara, ya kuma raba dubban mutane da gidajensu.

Hare-haren sun kuma mayar da mata sun zama shugabanni a gidaje, ya kuma mayar da yara da yawa marayu.

Kundin da WikkiTimes ta samu a Centre for Community Excellence, cibiyar da ke bibiyar adadin mutanen da aka kashe da dukiyar da aka rasa ya nuna cewa an kashe mutane sama da 3,000 a shekara biyun da su ka wuce.

An yi hasashen cewa an kashe Biliyan 1.2 a matsayin kudin fansa don sakar mutanen da aka yi garkuwa da su.

Kundin ya kuma nuna cewa an durkusar da kauyuka da garuruwa har 682, an kuma durkusar da harkokin tattalin arziki, abinda ya tilasta mutane barin garuruwansu da dukiyoyinsu.

Bayanan sun kuma nuna cewa maharan sun lalata gonaki sama da 2,706, sun sace shanu 13,883, sun kuma sace awakai da tumakai da adadinsu ya ka kai 11,088.

Mai son karanta wannan rahoto na musamman a harshen Turanci, sai ya ziyarci shafin www.wikkitimes.com

Turawa Abokai

2 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan