Al’majirci: Mathew Kukah ba shi da Laifi (1)

377

Almajiranci al’ada ce wadda ta samo asali daga addinin musulunci kuma ta zama wata hanya ta samar da malamai a cikin al’umma tare da gina kyawawan halaye da su ka hada da juriya, ingantaccen ilimi, tarbiya da biyayya.

A baya, al’umma ta ci moriyar almajiranci fiye da komai domin sakamakon ta ne Usmanu Bn Fodio ya kwato talakawa daga zaluncin sarakunan habe, kuma ya kafa daular Usmaniya wadda ta mulki kasashe a yammacin Afirka na tsawon shekaru dari.

Ni ganau ne, na yadda wannan tsari ke tafiya a shekarun baya domin na taso a gidanmu da almajirai, wadanda ba sa yawon barace-barace domin a cikin gidanmu su ke cin abinci da sauran bukatunsu.

Ban san iya yawan almajiran da mahaifina ya yaye ba, amma a wadanda na sani babu wani wanda ke daukar koko ya na yawon bara ko ya zama wani abu wanda iyayensa ko al’umma za ta yi tir da halayensa ba. Akwai cikin almajiran mahaifina, saboda kowannensu ya taso da wata sana’a, wadanda sun zama shahararru a sana’arsu.

Cikinsu akwai wanda idan ya yi maka gini za ka rantse da Allah shahararren architect ne ya zana.

Shaharasa a fannin gini ta kasance wasu manyan masu kudi a cikin kwaryar birnin Kano ba wanda za su bawa gini idan ba shi ba. Sannan akwai wanda ya zama hanshakin dan kasuwa da sauransu.

A yau almajiranci ya canza salo yadda duk wani abu na kirki da ka sani da su a da, sun kauce. Hakika yawanci iyayen almajirai da malamansu na yanzu za su kasance su ne silar shIgarsu wuta.

Dalili na a nan shine, iyaye na watsar da duk wani nauyi da Allah ya dora musu a kan yayansu su tura su wajen malamai wadanda ba za su iya dauke musu wani nauyi ba sai dai ma su dora musu na su. Akwai yaron da na gani wanda bai fi shekara shida ba cikin kwanakin nan kuma ya kasance ba ya gani, wato makaho ne.

Da na tambaye shi sai ya ce shekararsa kusan hudu a Kano kuma tun sanda aka kawo shi, wato bai fi shekara hudu ba kenan, har a lokacin da muka sadu babu wani wanda ya taba kawo masa ziyara daga gidansu balle ya tallafa masa ko sanin abinda ke ciki.

A daminar bara na sauko daga ofis dina da magariba na hangi wani yaro a gefen baranda cikin duhu yana kwance. Na iso inda ya ke na ga sauraye sun fi dari a yayyabe da shi amma barcinsa ya ke shirga. Da na tashe shi ya kai kimanin minti guda bai san inda kansa ya ke ba. A lokacin da ya dawo hankalinsa na tambaye shi ina ne makarantarsu, daga inda mu ke ya kai tafiyar kilomita biyar kuma tun safe ya ke yawo bai ci abinci ba.

Ya ilahi, ku gaya min ta yadda wannan yaron da ya kamata a ce kullum ya na kwance a bayan uwarsa, ya wayi gari ba abinda ya sani sai azabar yunwa da dauda da wahala kuma bai tashi ya san soyayya irin ta iyaye da yan uwa ba, ballantana ta sauran al’ummar gari, sannan babu ilimi na boko ko na arabi, ku gaya min a irin wannan tsari da ya taso, wa zai iya tausaya wa?

Kullum zai kasance cikin haushin sauran al’umma domin al’ummar ba ta tarbiyantar da shi cikin tausayi ba balle ya koya yadda shi ma zai tausaya mata. Idan ya dau bindiga ya na kama mutane don kudin fansa ko ya yi kisa don a biya shi, shin ba al’ummar ce ta tura shi cikin wannan yanayi ba?

Lokaci ya yi da za’a daina almajiranci gaba daya ko kuma a tabbatar an samar da sabon tsari, idan ba haka ba, masifu da za su zo nan gaba sakamakon samar da matasa wadanda ba su da tabbas a rayuwa ba wanda zai iya maganinsa. Mun ga yadda a kan yan kudade kalilan wani zai iya daukar bindiga ya kashe jama’a ko ya yi kunar bakin wake.

Dokar gwamnatin tarayya ta shekarar 2004 ta ilimin bai-daya ta baude kofa yadda aka shigar da gwamnatin tarayya wajen tallafawa karatun almajiranci. Ilimi wajibi ne kasa ta samar da shi akalla na shekaru tara ga yan kasa kuma a duk shekara kudaden da ake warewa hukumar ilimin bai daya ya kan zarta na kusan dukkan hukumomi.

Zamu kawo cigaban gobe insha Allah…

Daga Ali Abubakar Sadiq

Za’a iya riskar marubucin
08039702951
aleesadeeq1@yahoo.com

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan