Wasu da ake zargin ‘yan dabar APC ne sun kai wa Saraki hari a gidansa

160

A ranar Lahadin nan ne wasu da ake zargin ‘yan daban siyasa ne masu biyayya ga dan takarar gwamnan jam’iyyar APC a jihar Kwara suka kai hari gidan Shugaban Majalisar Dattawa, Dakta Abubakar Bukola Saraki dake unguwar Agbaji a Ilori, babban birnin jihar ta Kwara. Harin dai shi ne na biyu a cikin kwana hudu.

Wata sanarwa daga teburin yada
labarai na Saraki ta yi zargin cewa gungun ‘yan daban jam’iyyar APCn sun bude wa mazaunan unguwar wuta, inda suka jikkata a kalla mutum 11, sun kuma lalata kimanin motoci 50 da aka ajiye a wurare daban-daban a unguwar ta Agbaji.

Ko ranar Alhamis da ta gabata an yi zargin cewa ‘yan dabar na APC sun tada hankalin mutane a unguwannin Agbaji, Adewole da Pakta dake cikin birnin Ilori. ‘Yan jam’iyyar PDP hudu aka jikkata a harin.

Hakan ne ya sa Shugaban Majalisar Dattawa, Dakta Abubakar Bukola Saraki ya kira taron manema labarai a Abuja, inda ya yi ikirarin cewa rayuwarsa da ta iyalinsa da ta magoya bayansa tana cikin hadari.

A ta bakin mazauna yankin, harin ya afku ne da misalin karfe 11:30, inda maharan dauke da makamai suka fara harbin iska don tsorata mutane.

A ta bakin Shugaban Kungiyar Ci Gaban Agbaji, Alhaji Musa Olanrewanjo Yusuf, Yahya Seriki da Musbau Esinrogunjo su suka jagoranci gungun maharan.

Mista Yusuf ya ce an garzaya da mutane 11 din da suka samu raunuka zuwa Babban Asibitin Ilori da kuma wani asibiti mai zaman kansa.

“Yan daban APCn sun zo da misalin karfe 11:30 na safe, suka fara harbi ba kakkautawa a iska. A gaskiya, DPOn ‘yan sanda na Adewole ne ya ba su kariya.

“A kalla mutane 11 ne suka samu raunuka daga harbin bindiga, yayinda suka lalata kimanin motoci 50 har da ta Liman Aliagan”, in ji Mista Yusuf.

Ya kara da cewa sun kuma sace babura hudu, sun kuma sace kudade da kayan adon mata daga shagunan da masu su suka gudu.

Da yake tsokaci game da harin, Darakta Janar na Yakin Neman Zaben PDP a yankin, Farfesa Suleiman Abubakar ya ce jagororin APC a jihar su ne suke kunna wutar rikici don su jefa tsoro a zukatan jama’a tunda sun gane mutane sun dawo daga rakiyarsu.

Ya yi kira ga jami’an tsaro a jihar da su kama tare da gurfanar da wadanda suka kai harin na ranar Alhamis da na ranar Lahadi a gaban kotu.

Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar PDP a jihar, Tunde Ashaolu ya ce harin na ranar Lahadi ya tabbatar da ikirarin da Shugaban Majalisar Dattawa ya yi cewa rayuwarsa da ta iyalinsa na cikin hadari.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan