Ba za a kori Magu ba- EFCC

314

Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC ta karyata rahotannin dake cewa ana shirin korar Ibrahim Magu, Mukaddashin Hukumar daga aikinsa.

Tony Orilade, Mukaddashin Sashin Wata Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Hukumar ta EFFC, ya ce rahotannin kafafen watsa labarai dake cewa ana shirin korar Mista Magu daga aiki ba su da tushe ballai makama.

Mista Orilade ya bayyana haka ne a wata ganawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN a Abuja ranar Lahadi lokacin da yake mayar da martani ga wani rahoto dake cewa Fadar Shugaban Kasa na shirin korar Ibrahim Magu, Mukaddashin Hukumar ta EFCC daga aiki.

A cewarsa, Mista Magu ba ya son rahotannin marasa tushe daga kafafen watsa labarai su hana shi aiki.

“Ya dukufa kan yaki da cin hanci, kuma da yawa daga cikin ‘yan Najeriya da suke amfana da yaki da cin hancin na farin ciki da shi.

“Da yin nasarar kararraki 312 da ya hada da tsofaffin gwamnoni guda biyu da kuma wasu kararrakin biyar da aka shirya shigarwa a 2019, Hukumar EFCC karkashin shugabancin Magu ta cancanci yabo”, in ji Mista Orilade.

Wani rahoto ne a wasu kafafen watsa labarai ya ce wata kila a umarci shugaban na EFCC da ya tafi karo karatu don inganta aikinsa a Rundunar ‘Yan Sanda ta Kasa, inda tuni dama kwamishina ne.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN ya bada rahoton cewa fiye da shekara uku kenan Mista Magu yake a matsayin Mukaddashin Hukumar ta EFFC.

Sau biyu kuma Majalisar Dattawa tana kin tabbatar da shi a matsayin tabbataccen Shugaban EFCC.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan