Hukumar Wayar da kai ta ƙasa ta ƙaddamar gangamin wayar da kai akan zaɓe

400

Wannan gangami anyi shine a jihar Bauchi karkashin jagorancin Darakta Janaral na Hukumar Dr Garba Abari yadda ya bayyana irin matakan da hukumar ke dauka wajen Wayar da kan jama’a a daidai lokacin da ake shirin zaben 2019.

Darakta Janaral Wanda ya samu wakilcin daya daga cikin Daraktocinsa,yana mai fadin daukar wannan matakin ne domin tabbatar da zabe cikin kwanciyar hankali.

Shima da yake mai da jawabi ,Daraktan a jihar Bauchi, Alh Nuru Yusuf Kobi kiraye ga matasa dasu kaucewa tayar da yamutsi a lokacin zabe.

Alh Nuru Yusuf Kobi ya kuma yi amfani da wannan damar na shawartan yansiyasa dasu kaucewa siyasar a mutu ko ayi rai
Taron dai ya hade hancin jami’an tsaro,Masu rike da sarautun gargajiya da kungiyoyin fararen hula

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan