Sharhi: Anya Kwankwasiyya zata kai Labari Ba tare da Taimakon ‘Yan Tsohuwar PDP dake Karkashin Jagorancin Amb. Aminu Bashir Wali ba?

103

A satin da ya wuce ne, Kwankwaso yayi wa Dan Takarar Mataimakin Shugaban Kasa Mr. Peter Obi tare da Dan Takarar Gwamnan Kwankwasiyya Abba K. Yusuf Rakiya zuwa wajen ‘Yan Tsohuwar PDP dake Karkashin Jagorancin Amb. Aminu Wali a Gidan Sanata Bello Hayatu Gwarzo inda ya roke su dasu zubar da makaman su, su Kuma Dafawa ‘Yan Takarkarun sa domin Kaiwa ga Nasara a kakar zabe Mai zuwa. Nikam Sai na kasa Danne Dariya ta, da Mamaki na duk da Daman na Dade da hango zuwan irin wannan Rana, Ranar da Wanda ya nada kansa a mukamin “Sarki zai gwammaci Kasancewa Bafade”

Bari ma dai nayiwa Kwankwaso tuni. Hausawa na cewa Rana Dubu ta Barawo Rana Daya Tak kuma ta Maikaya ce, To wannan shine Matsayin Kwankwaso a siyasar Kano, Domin kuwa Dukkanin Alamu sun Nuna Karshen Siyasar Kwankwaso da kwankwasiyya ne yazo bayan zaben 2019.
A Fahimta ta, Tare da Dogaro da Tarihin Siyasar Kano, Kwankwaso ya amince ya fuskanci gaskiya da gaskiya ko ya iya tseratar da kungiyar sa ta kwankwasiyya daga Barazanar Rushewa, Karewa Tare da Shan mummunan Kaye a zabe Mai zuwa.

Duk da dai Ina ganin tuni Lokaci ya Kure masa, Amma al’amari ne a bayyane cewa PDP bazata iyacin zabe batare da Gudummawar ‘ Yan Tsohuwar PDP ba. Domin Tun Sanda Kwankwaso ya dawo cikin Jam’iyyar PDP Sai Kara Lalacewa take, Tana Kara Kanjamewa a sanadiyyar Kama karyar sa.

Abin Tambaya anan, shin Kwankwason ma da gaske yakeyi a wannan Sabuwar Aniyar tasa? Ko Kuma irin halayyar Nan tasa ce ta yaudara da kinaya? Domin kowa ya sanshi Bai yarda wani ya iya ba Sai shi. Ko kuwa dai Yana son yayi amfani da kuri’un ‘Yan Tsohuwar PDP wajen biyan bukatar kan sa ba tare da wani kwakkwaran Sulhu ko alkawari ba?

Abu ne a fili cewa Al’ummar Kano suna Kaunar Jam’iyyar PDP fiyeda Jam’iyyar APC Kuma a shirye suke su kayar da APC a zabe Mai Zuwa. To kodai Kwankwason Yana so yayi amfani da wannan dama ne Domin biyan bukatun kan sa?

Abinda mabiya Kwankwasiyya ya kamata su Gane akwai bambamci mabayyani tsakanin mutumin gari Wanda zai jefa Kuri’ar sa yayi tafiyar sa Gida da Kuma Dan Siyasa Gogagge, Jajirtacce Wanda zai iya amfani da hikimomi da dabaru da kowacce irin dama wajen samun Nasara a Lokutan zabe, Dan Siyasa guda daya Yana iya taka rawar da gungun Masu zabe Bazasu iya ba.

A jihar Kano, duk Mai bibiyar Harkokin Siyasa yasan cewa mafi yawancin jiga-jigan ‘Yan Siyasa Gogaggu Masu Karfin fada aji Suna tsagin Tsohuwar PDP Karkashin Jagorancin Amb. Aminu Bashir Wali, ka dauki shi kansa Jagora Amb. Aminu Bashir Wali Tsohon Ministan Harkokin kasashen waje, Tsohon ambasada Kuma daya daga cikin wadanda suka kafa Jam’iyyar ta PDP a kasa Baki Daya.

Akwai Sanata Bello Hayatu Gwarzo Wanda yayi Sanata sau Hudu a jere ba yankewa, Sanata Mas’ud El jibril Doguwa Shugaban Jam’iyyar PDP har sau biyu, Rt. Hon Ibrahim Salisu Buhari Imam Tsohon kakakin Majalisar Tarayya, Alh. Yahaya Bagobiri Gogaggen Dan Siyasa Mai Jama’a Kuma Shugaban Kwamitin kamfen na Dan Takarar Shugaban Kasa Alh. Atiku Abubakar, Mai Girma Sadiq Wali Matashin Dan Siyasa Mai kwazo da Hakuri, Jarumi Mai Taimako Wanda yayi Takarar Gwamna, Alh. Ibrahim Little Tsohon Dan Takarar Gwamna, Hon. Ahmad Mu’azu Hotoro Tsohon Shugaban karamar Hukuma Dan Siyasa Mai kwazo da kaifin basira Tare da tarin Magoya baya da wasun su da dama.

Ta Yaya zaka shiga filin daga batare da wadannan kwamandoji ba? Mai bin kwankwasiyya a makance zai iya tunanin Kwankwaso shi kadai zai iya wannan yakin, Duk da Hausawa Sunce Hannu Daya baya Daukar Jimka. Hasashen masana Siyasar Kano ya nuna cewa jam’iyyar PDP a Jihar Kano Tana cikin gagarumar Matsala irin wadda Bata taba shiga ba tun bayan kafata a shekarar 1998.

Daga: Muzakkir Rabiu Hotoro da Sani Saidu T/Wada.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan