Yadda Bikin tunawa da Ƴan Mazan jiya a Bauchi ya Kasance

38

An shawarci gwamnatin tarayya da Samar da makaman zamani ga sojojin Nigeria domin basu damar magance matsalar tsaron dake addabar wannan kasa

Shugaban kungiyar tsofafin sojoji na jihar Bauchi, Warrant Officer Idris Danjuma Ningi shi yayi wannan kiran a wajen bikin tunawa da yanmazan jiya daya gudana a dandalin taro na IBB Square, a Bauchi

Warrant Officer Danjuma Ningi ya kuma yi kiran sake bita was Fanshon tsofin sojojin domin gudanar da rayuwa cikin sauki

Dake mai da jawabi Gwamnan jihar Bauchi, Muhd Abubakar da ya samu wakilcin mataimakinsa Audu Sule Katagum yayi alkawarin goyo wa kungiyar Baya tare da basu tallafin motar Bus

Anyi fareti irin na sojoji tare da gudanar da addu’i na musamman domin tunawa da Jaruman da suka rayukansu a fagen daga.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan