Magoya bayan Buhari sun gigice bayan Ziyarar Atiku Amurka

258

Siyasar Najeriya na cigaba da daukar sabon salo gabannin zaɓen 2019. Tun bayan da ɗan takarar babbar jam’iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar ya ziyarci ƙasar Amurka jiya Alhamis.

Kafin wannan ziyara dai magoya bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari na yiwa Atikun da magoya bayansa zambo da cewa shi mai laifi ne da ake nemansa ruwa a jallo a ƙasar Amurkan, kuma da ya je zasu yi ram da shi.

Yayinda shi kuma Atikun a wata hira da BBC Hausa ya ce, ai ba wahayi aka yi cewa duk wanda zai mulki Najeriya sai ya je ƙasar Amurka.

To Amma a yadda siyasar Duniya ke tafiya yanzu da kuma irin alakar dake akwai tsakanin Najeriya da kasar Amurka, abu ne mai wuya a ce Shugaban Najeriya ba zai ziyarce ta.

Hakan ta sanya magoya bayan Shugaba Buharin suka matsaka kaimi wajen yada magana ga Magoya bayan Atikun tun da sukaa ga wurin lasa. Irin wannan faɗi in faɗa dai tafi tsamari a kafafen sada zumunta musamman na zamani wato faccebook da Twitter.

Ana cikin hakan ne shi kuma mai neman hamɓarar da Buhari a zaɓe mai zuwa a watan Fabrairu, yayi abinda ya bawa maras ɗa kunya, kwatsam sai ganinsa aka yi ya dira a ƙasar Amurkan.

Abin mamakin shi ne har yanzu babu labarin kama shi ko makamancin haka, wanda hakan ta sanya su kuma magoya bayansa suka fara mayar da martani gami da cewa “Yanzu kuma sai me, Atiku yaje Amurka.”

Atiku dai zai gana da ƴan kasuwar Najeriya dake can Amurka a yau Juma’a da maraice.

Yayin da anan gida kuma Sanata Shehu Sani ya zolayi magoya bayan Buhari a shafinsa na Twitter, inda yace yanzu kuma sai su koma cewa ai su ba haka suke nufi ba, cewa sukai sai ya je Sambisa.

Yanzu haka dai irin wannan muhawara na cigaba a shafukan Facebook da Twitter.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan