Dalilai 7 da suka sanya baƙi fifita Otal ɗin Bristol Palace kan sauran

303

Otal din Bristol Palace daya tamkar da dubu ne a cikin tsaransa, kamar dai kace masa murucin kan dutse baka fito ba sai da ka shirya.
An zubar da basira tun daga kan zabar garin da aka gina shi zuwa matsugunninsa, kana da yanayin lauyin da zubi da tsarin da aka yi masa wajen gini.
Bayan shafe sama da shekaru biyu da fara aiki, shi kadai ne Otal mai daraja ta biyar wato Five Star Hotel a baki daya yankin Arewa maso yamma, sannan idan ka cire babban birnin Tarayya Abuja babu jihar dake Otal tsaransa kaf yankin Arewacin Najeriya.
A yau mun zakulo muku wasu dalilai 6 da ya sanya baki fifita Bristol kan sauran Otal.
1- Cikakken tsaro ga lafiya da Dukiyar baki
A duniya yanzu kowa na saon ya samu tabbacin tsaron lafiyarsa da Dukiyarsa, hakan ta sanya Bristo tanadar kwararrun ma’aikatanta masu bayar da tsaro ga Baki da kayansu.

Sannan ga kuma jami’an ‘yan sanda a kusa domin tattabar da maganin duk wata barazana.
2- Karbar Baki cikin girmamawa da mutuntawa


A otal din Bristol, ana karbar baki cikin mutunci domin mun yarda cewa bakinmu su ne abin alfaharinmu, da su muke tutiya, don haka ne ake kyautata musu kamar suna dakunansu na gida koma fiye da hakan.

3- Dakunan kwana masu Numfashi

Wani kayan sai Amale ba dai Jaki ba, domin kuwa idanu ne kadai zasu iya tabbatarwa da kwakwalwa abinda ta gani. A Bristol, akwai dakunan kwana tsala-tsala kamar a Aljannar Duniya.

A kullum bakinmu sukan yaba da tsafta da kyawun kawar da muka yiwa dakunan saukar bakinmu, wannan ta sanya kowanne mutum ke burin saukar Bakinsa a Otal dinmu don fita kunya.

4- Daddadan Abinci mai rai da Lafiya

Dadin abincinmu kan sanya kunnuwa motsawa, domin kuwa mun tanadarwa abokan huldarmu abincin gida Najeriya da kuma na kasashen ketare ga masu sha’awar cin miyar makwabta. Dandanon sai wanda ya ci.

5- Wurin motsa jiki na zamani da babu kamarsa

A dakin motsa jiki kuwa lamarin ya bunkasa, baya ga kayan motsa jiki da karafunan nauyi don saisaita jiki da murdewa ga masu son kwanji,

mun tanadi kwararrun masanan da zasu baku shawarwari don cimma burin dalilin amfani da dakin motsa jikin namu.

6- Waurin Wanka mai Kyau Garai-Garai

Idan kayi ninƙaya a cikin wurin wankanmu (Swimming Pool) kai baka so fitowa ba, sakamakon kyawun ruwan tun a ido, da kuma yadda aka ƙawata shi.

Wani abin azo a gani da Bristol ya shallewa sauran Otal shi ne, duk girman ginin an tsara shi daidai da mutane masu buƙata ta musamman (Nakasassu) domin suma kar a barsu a baya.

Otal ɗin Bristol na da ma’aikata har 186, dake aiki ba dare babu rana 24/7.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan