Kisan kiyashin jihar Zamfara: Al’umomi na kokawa yayinda suke zargin ƴan siyasa, jami’an tsaro da sarakunan gargajiya da hannu (2)

434

A bangare na biyu na wannan bincike, Haruna Mohammed Salisu ya hada rahoto kan yadda ‘yan siyasa, jami’an tsaro da sarakunan gargajiya ke rura wutar rikici a hare-haren da maharan jihar Zamfara ke ci gaba da kaiwa a kauyukan jihar.

Mazuna kauyukan da maharan suka kai hare-hare, mutanen da rikicin ya raba da gidajensu, ‘yan kato da gora da kungiyoyin farar hula da jaridar WikkiTimes ta tattauna da su sun zargi shugabannin al’umma da na siyasa da laifin zubar da jinin da ake ci gaba da yi a dukkanin kananan hukumomi 14 dake jihar ta Zamfara.

Karanta Rahoton farkon kafin wannan cigaban na biyu.

Misali, wani mazaunin Maradun wanda ya yi magana da jaridar WikkiTimes bisa sharadin kar a bayyana sunansa, yayin da yake bayanin asalin rikicin ya danganta kisan kiyashin da yadda wasu ‘yan siyasa suka ba ‘yan daban siyasa muggan makamai a shekara ta 2011 a jihar da niyyar cin zabe ko ta halin kaka.

Koda yake dai jaridar WikkiTimes ba ta iya tabbatar da ikirarin nasa ba, mutumin ya ce wani mai suna Sani Gwamna Manyanci wanda a halin yanzu yana hannun jami’an tsaro sakamakon zargin sa da hannu a rikicin shi ne ya jagoranci maharan.

Wata majiya dake aiki da wata kungiyar farar hula a Gusau ta ce Sani Gwamna Manyanci shi kansa tsohon mai laifi ne wanda ya kulla wata alaka tsakanin gwamnatin jihar da maharan.

Mutane da dama sun yi amannar cewa alakar ta ba maharan damar samun karin makamai don kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, wadanda ba sa dauke da makamai.

“Gaba dayan abin munafunci ne. Ya za ka bada Miliyan Daya ga mai laifin da N400,000 ko N500,000 kawai ya kashe don siyan bindiga kirar AK47, idan ka yi haka, kana karfafa masa gwiwa ne ya kara kashe karin wasu mutane saboda za a saka masa sakamakon haka”, in ji Kwamared Munnir Haidara, Shugaban Majalisar Matasan Arewa, Reshen Jihar Zamfara.

Wasu mazauna Nasarawan Godal da rikicin ya raba da muhallinsu wadanda kuma suke da cikakken sanin yadda maharan suke aika-aika ya jaddada cewa Sani Gwamna Manyanci ne jagoran da ya wuce gaba wajen tsorata tare da tilasta masu zabe su zabi wasu ‘yan takara a zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC mai cike da rikici wanda ya sa jam’iyyar ta rasa dan takarar gwamna a zaben 2019.

“An yi mana barazana sosai, ‘yan daban siyasa sun daki wasu masu zabe wadanda tauraruwar siyasarsu ke haskawa sakamakon kin zaben dan takara kaza”, in ni wani daga karamar hukumar Birnin Magaji wanda ‘yan bangar suka dake shi.

Shi ma wani da abin ya shafa wanda aka kashe yayansa wanda ya dauki wakilanmu zuwa wasu kauyuka da sansanonin ‘yan gudun hijira a karamar hukumar Maradun ya tabbatar da cewa an ga Sani Gwamna Manyanci kuru-kuru rike da bindiga kirar AK47 a tsakanin maharan a shekara ta 2017 a dajin Mahanga, daya daga cikin maboyar maharan.

Haka kuma, wasu mazauna karamar hukumar Tsafe wadanda suka tattauna da wannan jarida sun ce an tsorata su, an kuma tilasta musu zaben wani dan takara, ko kuma a ‘saka musu da harsashi’.

Lokacin da WikkiTimes ta jefa tambaya ga Jami’in Hudda da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Zamfara, ASP Mohammed Shehu game da Sani wanda rahotanni suka ce Rundunar ta kama shi, sai ya ce: “Ba zan iya tsokaci akan wannan ba, ban san abinda ka ke magana akai ba, ban san abinda ka ke cewa ba”.

Mazauna karkara da harin maharan ya shafa ba su kadai ke nuna wa ‘yan siyasa yatsa ba musamman shugabannin siyasa na yanzu da makusantansu.

Misali, Adamu Abubakar, Shugaban Centre for Community Excellence ya yi mamakin dalilin da yasa gwamna ya yi watsi da gargadin tsaro tun farkon fara rikicin. Kungiyoyin fararen hula sun dade suna yi wa gwamnatin gargadi, amma ya yi alhinin cewa an siyasantar da gargadin nasu a matakin farko ta hanyar tarukan manema labarai dake karyata gargadin da kuma dukkan nau’o’in farfagandar kafafen yada labarai.

Ya ce gwamnati ba ta son daukar matakai don kawo karshen rikicin, yana mai yin tambayoyi da dama kan ko suna da sha’awar zubar da jinin da ake yi.

Adamu ya ce babbar manufar kowace gwamnati a duniya shi ne ta kare rayuka da dukiyoyin al’ummarta, idan suka kasa yin haka, sun rasa iko, a al’amarin jihar Zamfara, an samu cikakken tasgaron bin tsarin mulki wajen gudanar da ayyukansu.

“Ya kamata a ce gwamnan yana yin taron ganawa da dukkan jami’an tsaro a duk ranakun Laraba na mako, amma ka tuna, ya fada wa duniya cewa shi fa yanzu ba shi ne jami’in tsaron jihar ba”, a kalaman Adamu.

Wani mamba na wata kungiyar farar hula a jihar wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya ce: ” Ko jihar Borno da ita ce jiha mafi muni da ‘yan Boko Haram suka kai hari, gwamnan bai ajiye mukaminsa na jami’in tsaron jihar ba, ya tafi da yanayin duk da a wancan lokacin shi ba abokin shugaban kasa mai ci ba ne.

“Akwai tambayoyi da yawa da ya kamata gwamna mai ci ya amsa idan an zo maganar kashe-kashen da ake yi a jihar”, in ji Adamu.

Haka kuma, Shugaban Majalisar Matasan Arewa, Reshen Jihar Zamfara, Kwamared Munnir Haidara shi ma ya zargi gwamnan jihar da yin wasarairai da harkokin tsaro a jihar tun shekara ta 2011 lokacin da rikicin ya fara.

Kwamared Munnir ya ce sun nusar da gwamnan, sun kuma yi taron ganawa da shi da rubuta jawaban bayan taro, ya ce amma kamar gwamnati ba ta da sha’awar kawo karshen rikicin.

Munnir ya ce gwamnan ya yi watsi da duk gargade-gargade da manya-manyan masu ruwa da tsaki da ya hada da jami’an tsaro suka yi masa.

“Gwamnan ba ya ma zama a jihar, ba ya yin tarukan ganawa akan tsaro, yakan yi tafiya ba ya nan ba ya can yayin da jihar ke ci da wuta”, in ji Munnir.

Lokacin da wannan dan jarida ya tambayi Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Zamfara game da ko suna yin tarukan ganawa da hukumomin tsaro a jihar sai Jami’in Hudd da Jama’a na Rundunar ya ki ya ce komai akan haka. Ya ce: “Ka ga, bari in fada maka, kawai ka takaita kanka akan wannan, cewa mu Rundunar ‘Yan Sanda muna da kyakkyawar alaka da gwamnatin jihar, kuma wannan shi ne zahirin abinda nake so ka fahimta, kuma wannan shi ne gaskiyar al’amarin”.

Wani jami’in kato da gora a daya daga cikin kananan hukumomin da WikkiTimes ta ziyarta ya ce danganta tsakanin ‘yan siyasa da ‘yan fashin a fili take.

Wannan majiya ya bayyana cewa akan janye jami’an tsaro daga wuraren da ‘yan fashin ke son yin fashi don ba su damar yin fashi ba tare da cikas ba, sukan ba su gudunmawar muggan makamai, sukan bukace su da su razana masu zabe don zabar dan takararsu ko kuma su kashe su.

WikkiTimes ta kira waya tare da aika rubutaccen sako ga Ibrahim Dosara, mai magana da yawun Gwamna Abdul’aziz Yari, amma bai dauki kiranmu ba ko sake kiran mu don yin tsokaci game da zargin da ake yi wa shugaban nasa.

Rawar da jami’an tsaro ke takawa a rikicin
Haka kuma, majiyoyi da dama sun zargi jami’an tsaro da taimaka wa ‘yan siyasa don cimma mummunar manufarsu.

Wani jami’in tsaro mai ritaya wanda ya yi magana da WikkiTimes a karamar hukumar Maradun ya ce ‘yan siyasa sukan hada baki da jami’an tsaro don sakin ‘yan fashi idan jami’an tsaron sun kama su.
Mazauna a mafi yawan kauyukan da abin rikicin ya shafa sun ce jami’an tsaro nada hannu ta yadda suke barin ‘yan fashin su ci karensu ba babbaka, kuma suna dari-darin fuskantar su.

Misali, Abu daga Falau (an boye ainihin sunansa da garinsa), wani dan kato da gora wanda ya dauki wakilinmu akan babur zuwa wurare a daya daga cikin kananan hukumomin da suka ziyarta ya ce: “Idan muka shirya aikin hadin gwiwa da jami’an tsaro, sai su janye da zarar sun ji karar bindigar maharan”.

“Wani lokaci sai su ce mana motarsu ba fitila, saboda haka dole su janye, ko da rana kata za su iya janyewa, kuma su ce maka umarni ne daga sama”, suka bar shi yana tunanin me “umarni daga sama yake nufi”.

Mambobin kungiyoyin fararen hula a jihar da mazuna kauyukan da rikicin ya raba da muhallinsu wadanda suka san aikace-aikacen jami’an tsaro sun shaida wa wannan kafa cewa hukumomin tsaron ba su da sha’awar kawo karshen kisan kiyashin jihar ta Zamfara.

Misali, wasu mazauna karkara sun ce an bada sunayen wasu jami’an ‘yan sanda masu mukamin ASP da DPO a matsayin wadanda suke kawo wa maharan albarusai. Mazauna garin Nasarawan Godel sun fadi sunan wata jami’ar ‘yar sanda mai suna ASP Binta wadda suka ce abokiya ce ta kut da kut ga maharan. Har lokacin hada wannan rahoto, WikkiTimes ba ta iya tabbatar da ikirarin nasu ba.

“Bari in fada maka, su (suna nufin jami’an tsaron) ba sa son kawo karshen rikicin. Jami’an tsaron sun san dukkan sansanonin maharan, sun san shugabanninsu, wadannan masu laifi ba aljanu ba ne, kowa ya san su, musamman ma jami’an tsaro, kawai dai ba sa so su kawo karshen rikicin ne”, a cewar mazauna kauyukan.

Lokacin da wannan dan jarida ya fada wa Jami’in Hudda da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Jihar ta Zamfara, ASP Mohammed Shehu damuwar wadannan mazuna karkara cewa jami’an tsaron sun san maharan da maboyarsu kuma ba sa son kama tare da gurfanar da su a gaban shari’a, ya tabbatar da da cewa jami’an tsaron suna sane da maboyarsu.

“Mahanga kusan ita ce maboya mafi girma a duk fadin jihar Zamfara”, in ji jami’in.

Ya ce wata rundunar tsaro ta musamman ta je maboyar maharan ta kuma kashe fiye da mahara 104, ta kuma lalata sansanoni da dama, ikirarin da da yawa daga cikin ‘yan kato da gorar ba su yadda da shi ba, duk da rahotannin kafafen watsa labarai.

“Idan da sun yi nasarar lalata sansanonin, me yasa kashe-kashen ya ci gaba”?, daya daga cikin majiyoyinmu ya yi tambaya.

Kusan babu jami’an tsaro a wuraren da abin ya shafa
A dukkanin kananan hukumomi hudu da WikkiTimes ta ziyarta, kusan babu jami’an tsaron a wuraren da rikicin ya shafa. Bincike ya nuna cewa jami’an ‘yan sanda suna shelkwatocin kananan hukumomi ne kawai, hakan ya mayar da kauyuka ba masu kawo musu taimako daga maharan da kusan ke kai hari da kariya.

Daga Gusau, babban birnin jihar zuwa Birnin Magaji, mahaifar Mansur Dan-Ali, Ministan Tsaro na Najeriya, tafiyar kilomita 104, shingen ‘yan sanda daya ne kawai wanda yake kusa da wani ofishin ‘yan sanda a karamar hukumar Kauran Namoda.

Daga Gusau zuwa karamar hukumar Maradun wanda ya fi nisan kilomita 76, wakilinmu ya ga shingen tsaron soji guda daya ne kawai, shi ma kuma yana kusa da shelkwatar karamar hukuma ne.

Daga Yankara, wani gari da yake bakin iyakar Katsina da Zamfara, da kuma daga Tsafe zuwa Gusau, jami’inmu ya ga shingen tsaron hadin gwiwa na jami’an kula da shige da fice da sojoji guda daya ne kawai. Haka kuma, babu shingayen tsaro daga Tsafe zuwa Gusau, nisan kilomita 46.

Kusan a dukkan al’umomin da wannan kafa ta ziyarta, a fili yake cewa babu jami’an tsaro, abinda ke tilasta kafa kungiyoyin ‘yan kato da gora don bada tsaro na wucin gadi, jami’an tsaro sau da dama sukan gudu saboda manya-manyan makamai da maharan ke da su.

Wani direba da yake zirga-zirga tsakanin Tsafe zuwa Gusau da kuma Gusau zuwa Maradun ya yi mamakin me yasa aka cire shingayen jami’an tsaro aka kuma kwashe jami’an tsaro daga wurare masu muhimmanci.

Lokacin da WikkiTimes ta yi tambaya me yasa aka cire shingayen jami’an tsaron ba kamar sauran wuraren da rikici ya addaba ba inda mutum zai iya ganin an kafa shingayen tsaro da dama a muhimman wurare ta yiwu don dakatar da zagayawar makamai da kama masu laifi, sai Jami’in Hudda da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan ya ce: “Wata kila ‘yan sanda za su rika amsa kiraye-kirayen waya na gaggawa”.

Amma majiyoyi da dama daga kauyukan da rikicin ya shafa wadanda suka yi magana da WikkiTimes sun yi wani zargi na daban. “Ba mu amince da jami’an tsaron ba, akwai shingayen tsaro da motocin sintiri da yawa akan mafi yawan hanyoyin nan kafin a fara rikicin.

Amma shingayen tsaron sun bata a lokacin da aka fi bukatar su”, wani direba da ya saba da zirga-zirga da jirgin kasa a jihar ta Zamfara ya fada wa fasinjoji da suka hada da wakilinmu dake cikin jirgin zuwa karamar hukumar Maradun haka.

Ƴan kato da gora sun koma yin amfani da maganin bindiga don fuskantar mahara amma suna tsoron masu bada bayanan sirri

Lokacin da wakilinmu ya tambayi ‘yan kato da gora yadda suke fuskantar maharan da suke bayyana dauke da isassun makamai kuma cikin karsashi, sai Ali Manu, wani dan kato da gora daga karamar hukumar Tsafe ya ce: “Maganin bindiga yake taimakon mu mu kauce wa albarusai, wannan shi ne kadai tsaronmu a halin yanzu”.

Lokacin da wannan dan jarida ya hau abin hawa daga karamar hukumar Maradun zuwa Gusau, fasinjoji sun samu batun tattaunawa, rawar da magungunan bindiga ke takawa wajen zaburar da ‘yan kato da gora wajen bada tsaro ga kauyukansu.

Lokacin da wannan dan jarida ke tattaunawa da wata majiya daga kauyen Tsabre a karamar hukumar Birnin Magaji wanda yake bada labarin wahalar da suka sha, sai ga wata mata ta bayyana, dole mutumin ya tsaya da bada bayani.


Bayan dan wani lokaci da kowa ya yi shiru, sai matar ta tambaya wane ne dan jaridar, sai majiyar ya ce dan jaridar abokinsa ne daga Gusau.
Ta dan tsaya, ta harari dan jaridar sannan ta tafi.

Sakamakon bincike da WikkiTimes ta samu sun nuna cewa ana zargin matar ita ce mai samar da bayanan sirri ga maharan game da mazauna karkara da suka bijire, tana bayyana sirrinsu ga jami’an tsaro ko mutane daga waje.

Koda yake ita ma ta ruga da gudu don tsira da ranta lokacin da maharan suka kai hari a kauyen Tsabre, amma sauran ‘yan gudun hijira ba sa amincewa da ita.

Ana zargin sarakunan gargajiya, an tumbuke wasu

Ana zargin sarakunan gargajiya su ma nada hannu a rikicin ta hanyoyi da dama, sukan ba maharan kariya, sukan taimaki ‘yan siyasa wajen rage girman matsalar, sukan tilasta mutane a gidaje su karbi ‘yan gudun hijira don guje wa jibge su a sansanoni, don saukaka hana bazuwar bayanai game da rikicin.

Misali, a karamar hukumar Birnin Magaji, mahaifiyar Mansur Dan-Ali, Ministan Tsaron Najeriya, ‘yan gudun hijira daga Tsabre, Garin Kuka da Garin Haladu da maharan suka raba da muhallansu an yi musu sansani ne a Makarantar Firamare dake Galadima, a watan Nuwamba da Disamban 2018, biyo bayan wasu mabanbantan hare-hare guda biyu.

Nisan Makarantar Firamare ta Galadima da gidan da aka haifi Ministan ‘yan mitoci ne, kuma tana kusa da Fadar Sarkin Garin.

Mazuna kauyukan da rikicin ya raba da gidajensu sun zauna a cikin makarantar ne tsawon kwana uku kawai, “an kuma rarraba su a tsakanin gidajen garin don gudun kunyata”, in ji Sunusi, wani mazaunin karkara da rikicin ya raba da gidansa daga Tsabre, maharan kuma sun kashe masa ‘ya’yansa uku.

Lokacin da wannan dan jarida wanda yake badda kama a matsayin ma’aikacin jin kai ya matsa don gano me yasa aka fitar da ‘yan gudun hijirar daga Makarantar Firamare ta Galadima, sai Sunusi ya sha jinin jikinsa bayan da ya lura da wasu bambance-bambancen harshe. Daga bisani dai sai ya ki yin magana, ya bar wajen da sauri ya bar wannan dan jarida da mai yi masa jagora a makarantar.

Lami, (ba sunanta ne na gaskiya ba) daga Ruwan Bado take a karamar hukumar Maradun. Mijinta ya sake ta, kuma ya bar ta ta kula da tacwayenta da sauran ‘ya’yanta guda biyar. Ita ma ta zargi Sarkin garinta da hannu a rikicin. “Kafin mijina ya tafi, ya fada mana yadda Sarkinmu ya rika taimakon maharan da bayanai don su ci gaba da yi mana ta’addanci. Amma ba za mu iya cewa ko shi ma yana yin hakan ne don tsoron kada maharan su kashe shi ba” a kalamanta.


Wata majiyar ita ma wadda ta bukaci a sakaya sunanta ta zargi Sarkin Birnin Magaji, Alhaji Hussain Dan-Ali da fitar da ‘yan gudun hijirar daga Makarantar Firamaren ala tilas don “guje wa kunyata ga Ministan”.

Majiyoyi a karamar hukumar sun ce Sarkin yana aiki ne da “umarni daga sama” don hana bazuwar bayanai game da ‘yan gudun hijirar a karamar hukumar.

Samun damar yin magana da karin wasu wadanda rikicin jihar ta Zamfara ya shafa ya zama wani aiki mai matukar wahala.

Misali, duk da badda kama da wannan dan jarida yake yi a matsayin ma’aikacin jin kai dake kokarin samun alkaluman wadanda suka rasa gidajensu don ba shi damar kawo kayayyakin agaji ga ‘yan gudun hijirar dake shan wahalar zuwa wasu gidaje a Birnin Magaji, alama ce dake nuna cewa an ajiye su ne a makarantar don hana baki samun damar shiga.

Da taimakon mai yi wa wannan dan jarida jagora, WikkiTimes ta samu damar shiga wani gida dake dauke da ‘yan gudun hijira su 25 a karamar hukumar ta Birnin Magaji. Lokacin da wannan dan jarida ya shiga gidan, ya kirga yara 14 masu mabanbantan shekaru da idonsa, suna jiran iyayensu su gama girki, saboda za a iya ganin alamar yunwa da damuwa a tare da su.

Wannan dan jarida wanda aka kalle shi sosai ba a ba shi damar daukar hotuna ba, amma cikin lura ya dauki mazauna kauyukan hotu ba tare da saninsu ba.

A baya dai gwamnatin jihar ta sauke sarakuna bakwai sakamakon zargin su da ake da taimakawa maharan.

Boye matsalar yana hana aikin ceto
A ranar Laraba, 26 ga Disamba, 2018 da sassafe a Nasarawan Godal dake karamar hukumar Birnin Magaji, wannan dan jarida ya shaida yadda aka shigo da mata ‘yan gudun hijira zuwa garin daga makobtan kauyuka da ‘ya’yansu kanan da ‘yan kayayyakin da za su iya dauka yayinda suke guje wa gungun maharan.

Maharan sun kai hari ga dukkan kauyukan dake yankin. Wasu mata wadanda ana ganin su suna cikin damuwa da rudewa sun fada wa WikkiTimes cewa maharan sun kona kauyukansu, kuma tunda aka fara jerin hare-haren, ba su samu wani tallafin jin kai daga kowa ba, duk da cewa maharan kusan sun kwace musu komai.

Adamu Abubakar daga Kwatarkwashi ya yi bayanin abinda yasa ba a samu tallafi ba ga wadanda rikicin ya shafa. “Gwamnatin ba ta son duniya ta san wani abu yana faruwa a Zamfara, idan kana boye matsalolinka na kanka, ya ka ke tsammanin mutane za su zo su taimake ka”.

Kokarin rage girman matsalar da watsi da ‘yan gudun hijirar shi yasa suka yi wata zanga-zangar tashin hankali da ta sa aka kona sakatariyar karamar hukumar Tsafe kurmus.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan