Home / Addini / Za a sa wa filin jirgin saman Louisville sunan Muhammad Ali

Za a sa wa filin jirgin saman Louisville sunan Muhammad Ali

A ranar Laraba, 16 ga watan Janairu, 2018, hukumomi a birnin Louisville dake jihar Kentucky a kasar Amurka suka ce za su sake wa filin jirgin saman dake birnin suna, inda za su sa masa sunan shahararren dan wasan dambe kuma mai aikin jin kan nan na duniya, Muhammad Ali, kamar yadda mujallar Courier Journal ta bada rahoto.

A yanzu za a rika kiran sa da Filin Jirgin Saman Kasa da Kasa na Muhammad Ali dake Louisville.

“Muhammad Ali na duniya ne, amma yana da mahaifa guda daya kawai, kuma aka yi sa’a ita ce babban birninmu na Louisville”, in ji Magajin Gari, Greg Fischer.
Muhammad Ali dai dan wasan dambe mai kuma aikin jin kai wanda duniya ba za ta manta da gudunmawarsa a bangaren wasanni da aikin jin kai ba.
A ranar 3 ga watan Yulin 2016 ne babban dan birnin Louisville, Muhammad Ali ya rasu sakamakon fama cutar ciwon gabbai tsawon shekaru 30.

Har lokacin rasuwarsa, Muhammad Ali ya yi kokarin ya ga cewa duniya ta zauna cikin soyayya, zaman lafiya da fahimtar juna.

About Labarai24

Wannan Jarida ce ta shafin Intanet dake kawo muku labarai da rahotannin. har da Bidiyo da Audio.

Check Also

Banyakole: Garin Da Mahaifiya Ke Kwanciya Da Mijin ‘Yarta

Yawanci rawar da ƙanwar mahaifiya ke takawa shi ne nuna soyayya tare da shiryar da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *