Buhari ga Obasanjo: Zan koya maka darasin siyasar da ba za ka taba mantawa da shi ba

204

Shugaba Muhammadu Buhari ya ci albashin koya wa tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo da “abokan tafiyarsa” darasin siyasar da ba za su manta da shi ba, a cewar jaridar The Cable.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Kasa, Garba Shehu ya fitar a madadinsa, Buhari ya zargi tsohon shugaban kasar da zama makiyin shugabannin da ba ya iya juya su.

Ya bayyana shi a matsayin wanda ba shi da ikon sukar gwamnatinsa.

An fitar da sanarwar ne a matsayin martani ga sukar da Obasanjon ta baya bayan nan.

Obasanjon dai ya yi zargin cewa Shugaba Buhari yana mayar da kasar kamar yadda tsohon shugaban mulkin soja, Sani Abacha ya yi.

Da yake karyata zargin, Shehu ya ce Obasanjo yana bukatar ya je asibiti don a duba lafiyarsa.

“Wasikar mai shafi 16 da tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya rubuta wa Shugaba Muhammadu Buhari aka kuma sake ta da yammacin nan ita ce yunkuri na karshe na ‘yan siyasar dake son karbar mulki ko ta halin kaka, wadanda ba za su iya juya Shugaban Kasar ba a siyasance, sun kuma koma karya”, in ji sanarwar.

Sanarwar ta bukaci tsohon shugaban da ya je ya ga kyakkyawan likita don samun kyakkyawar kulawa, ta kuma yi masa fatan samun sauki cikin gaggawa.

Sanarwar ta ce tun lokacin da Cif Olusegun Obasanjo ya bar mulki a shekarar 1979, bai kyale duk wani shugaban dake samun nasara ba ya yi aikinsa sosai.

“Abinda Cif Obasanjo da shi da abokan tafiyarsa a jam’iyyar PDP za su yi tsammani shi ne daga sakamakon zaben, za mu koya musu darasin siyasar da ba za su taba mantawa da shi ba”. Wannan banbancin zai fi na shekarar 2015″, a kalaman Mista Garba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan