Buhari Ya Bada Umarnin Gurfanar Da Babachir Lawal

236

Mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo ya ce, shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarnin gurfanar da tsohon Sakataren Gwamnatin ƙasar nan, Babachir Lawal saboda zargin sa da handame kudaden da aka ware domin agaza wa ‘yan gudun hijirar Boko Haram.

Osinbajo ya ce, shugaba Buhari ya bukaci Hukumomin Yaki da Cin Hanci da Rashwa da su shirya tuhumar Lawal wanda aka sauke daga mukaminsa a ranar 31 ga watan Oktoban shekarar 2017.

Wannan na zuwa ne bayan caccakar da ake yi wa gwamnatin Buhari na jan-kafa wajen gurfanar da Lawal, yayin da rahotanni ke cewa, yana cikin ‘yan sahun gaba da ke yi wa Buhari yakin neman sake zaben sa.

Har ila yau, shugaba Buhari ya bada umarnin gurfanar da tsohon Darekta Janar na Hukumar Leken Asirin kasar, Ayodele Oke wanda shi ma ake zargi da aikata almundahana.

An samu tarin dukiyoyi a wani gida da ke unguwar Ikoyi a jihar Legas, kudaden da ake danganta wa da Mr. Oke.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan