Ƙabilar Hausawa suna zauna ne a sassan nahiyar Afrika ciki har da arewacin Nigeria, kuma mafiya yawansu Musulmai ne da kuma mabiya addinin Kirista, wanda basu kai musulmai yawa ba.
Aure a kasar Hausa, ko wacce Kabila suna bin koyarwar addinin sune da kuma al’ada wanda a Nigeriya muna da manyan kabilu guda uku da suka hada da: Hausa, Igbo da kuma Yoruba. Kabilar Hausa tana da nata tanadin na auratayya da kuma koyarwar addini.
Saurayi in ya hadu da budurwa, da fari yana neman izinin iyayenta domin bashi damar aurenta. Su kuma iyaye suna gabatar da bincike akan waye shi kuma, daga ina ya fito gudun kar ayi kitso da kwarkwata, wannan yana faruwa ne a ko wacce Kabila a Nigeriya domin duk wanda ya aurar da yarsa burinsa ta zauna lafiya, shiyasa aure yake farawa da wasu matakai na al’ada. A wasu shekaru da suka gabata a baya ana bawa saurayi budurwa saboda iyayensa, duba da karamcin su, da sauran wasu kyawawan halaye nasu.
Domin kuwa da a kasar Hausa iyaye sune suke hada aure kuma a zauna lafiya babu maganar fada ko saki, yanzu kuwa samari sune suke zabowa kansu matan da suke ganin sunyi dai dai dasu, kuma daga baya auren babu wata dadewa da yakeyi, sai a rabu, banbancin wannan auren da na baya, na yanzu akwai soyayya, na da kuma babu maganar soyayya sai ma jin kunyar juna da akeyi. A tunani na auren da akayi soyayya kamar zaifi zama lafiya domin kuwa kowa ya fahimci halin kowa, haka zai zama hanya mafi sauki na zaman aure lafiya. Amma duk da wannan damar da ake samu na zance a Kasar Hausa ana samun karuwar mutuwar aure.
Mai yasa ake samun karuwar mutuwar aure a kasar Hausa, a nazarin da masana halayyar dan Adam su kayi (SOCIOLOGISTS), Zan fara da masani (Kantz 1992), ya Kalli aure, wata hanya ce wadda mace da namiji suke bi domin samar da al’umma wadda take an fanar wa domin samun mutane na gari. Haka shima masani (Bohannan 1970), yace wata alakace mai karfin gaske ake daurawa tsakanin mace da na miji, da kuma dokoki a tsakanin su da bawa kowa dama, masanin yace zama ne mara yankewa har sai lokacin da mai rabawa ta raba. In na gane mai masani yake nufi anan duk wanda sukai aure babu fatan rabuwa kenan sai dai mutuwa ta raba.
Sakin aure ya zama ruwan dare a tsakanin al’ummar kasar Hausa, kuma yana zama bara zana ga mata da basu da aure, kanfanin jaridar da take fita lahadi-lahadi, (Sunday trust), ta fitar da wani bincike da ta gabatar a April 3rd 2007, wanda yake nuna cewa kaso 80% na ma’aurata a jihar Kano, auren bashi da karko. Duba da yadda ake samun karuwar mutuwar auren. Haka suma masana da kungiyoyi suke ta fafutuka domin ganin an rage yawaitar mutuwar aure. Wata kungiyar zawarawa da marayu, Voice of windows, Divorces and orphans association of Nigeria. (VOWAN), wadda aka kafa ta a shekarar (2004), ta kaiwa majalisar dokoki ta jihar Kano. (State House of Assembly), ziyara a shekarar 2007 29th January, domin neman majalisar tayi doka na rage mutuwar aure a jihar. Amma har yanzu shiru kakeji kamar Malam yaci shirwa.
Duk da ina sane da cewa talauci yana bada gudunmawa wajan karuwar mutuwar aure a wannan lokacin, amma haka ba yana nuna cewa zai zama hujja ga karuwar mutuwar auren ba, saboda duk wanda ya auri mace to duk wani hakkin ta ya rataya a wuyansa. Wannan nauyi da ake magana ya zama dole akan mijinta ba ganin dama bane. Sakin aure ya kasu rukuni daban daban, akwai rukunin matan da basa daga cikin wanda aurensu yake mutuwa, ba ina nufin basa rabuwa da mazajansu ba amma dai da wahala kaga wannan matan sun rabu da mazajansu na aure.
Karamin abu yana kawo mutuwar aure. Maza suna kiran mata da marasa hankali, da gaya musu bakaken maganganu wannan duk ya saba da halayyar dan Adam. Amma yanzu dama kowa ya samu na yayi abinda ya ga dama da kansa, ya kamata yanzu Kotu ta rage karbar Shariar auren da bashi da sheda, ina nufin (marriage certificate), Malamai da Sarakuna da suke kusa da talaka, suke bada shawara lokacin daurin aure, ga ma’aurata domin rage karuwar mutuwar aure.
Ko wacce al’umma tana da irin dokar da zatayi akan aure a wannan lokacin. Duba da gwamnati ba abin da yake gabanta kenan ba. Ya ragewa al’umma suyi tsarin da zai kawo raguwar mutuwar aure a kasar Hausa.
Masu cewa baza a kyautatawa mace ba, wannan bahagon tunani ne da bai kamata ace ana wannan tunanin ba yanzu. Dalili kuwa hakkin mace da yake kan mijin ta yafi yawa akan hakkin sa da yake kanta.
Lokacin muzgunawa mace ya wuce ko bata mata rai, babu abinda ya kai mace saukin sarrafawa a cikin al’umma in dai akwai kyautatawa.
Dalilin rubutunnan shine mai yake kawo karuwar mutuwar aure? wacce hanya za abin domin rage faruwar matsalar? abu na farko shine neman ilimin sanin mai nene auran kansa? mai addini yace akan aure? mai al’ada take magana akan aure? abu na biyu neman matar da tayi dai dai da auranka, misali duk wanda ya auri mata tayi sama da samun sa akwai yiyuwar zasu iya rabuwa duba da rashin samun abinda take samu a gidansu, abu na uku bata dama na wasu uzirin gabanta domin dan adam ko wanne lokaci yana zaune a waje daya akwai ta kura da kuncin rayiwa ko da kuwa ace in da take ya kai girman filoti (5), na hudu kula da matsalolinta da nuna mata kauna da yaba mata. Yara suna zama koma baya da rasa wani jin dadi na rayuwa lokacin da aka rabasu da iyayensu ta hanyar saki.
Hanyoyin da za’a bi domin magance matsalar karuwar sakin aure. Gyara tsarin neman aure, rage bawa yan mata damar tara samari da yawa da sunan tana da farin jini.
Daga
Shuaibu Lawan
shuaibu37@gmail.com
08037340560 Saƙo Kawai (Text Only)
Zanci gaba insha Allah.