Za’a Gudanar Da Jarrabawar Tantance Imani A Sweden

164

Ƙasar Sweden ta yanke shawarar gudanar da Jarrabawar tantance Imani dominn tantance Kiristan Gaskiya da kuma Baragurbi a sahun dubban ‘yan Afganistan da suka yi ridda dominn rungumar Kiristanci da nufin samun damar rayuwa a kasar.

Ma’aikatar shiga da fice ta Sweden ce ta kuduri aniyar gwada imanin sama da mutane dubu 20,000 (yawancin su ‘yan Afganistan) wadanda suka tabbatar wa gwamnatin kasarsu ce sun yi watsi da addinin Musulunci domimn rungumar Kiristanci.

Cikin wani rahoto da jaridar Aftonbladet, ta bayyana cewa ma’aikatar shige da fice ta kasar ta ce sun gwada imani sama da matasan masu neman mafaka dubu 20,000 wadanda yawancin su ‘yan kasar Afganistan ne, kafin sun amince da su da kuma basu izinin ci gaba da rayuwa a kasarsu.Saboda sun sanar musu da cewa sun sauya addinin daga Musulunci zuwa Kiristanci

Rahotannin sun tabbatar da cewa, an kori illahirin wadanda suka fadi a wannan jarabawar daga Sweden, abinda yasa nan take wani hamshakin marubuci na kasar, Edward Blom ya fitar da wata sanarwa a shafinsa na sada zumunta kamar haka: “Kashi 43 cikin dari na amsoshin da aka tambaya ne kawai na amsa”.

A gefe daya kuma, babban malamin cocin yankin Skaraborg, Ake Bonnier ya nuna bacin ransa a tashar talabijin SVT taare da sukar lamirin ma’aikatar shiga da fice ta Sweden, inda ya ce” Wannan ai tsagwaron wauta ce. Ni kan kaina a matsayin na babban malamin coci akwai tamboyin da dama da na kasa amsawa. Shin ma’aikatar shiga da fice za ta kore ni daga kasata ?”.

Bayan yawaitar cece-kuce kan wannan lamarin mai ban ta’ajibi ma’aikatar ta fitar da wata sanarwa ta musamman, inda ta ce babu wata jarrabawar tantance imani ga “Yesu Almasihu” da ta taba gudanarwa.Wadannan maganganun karyace- karyace ne marasa tushe balantana asili.

Amma ma’aikatar ta sanar da cewa, ta yi wa wasu masu neman mafaka da ke neman izinin ci gaba da rayuwa a kasarsu,wasu tambayoyi kan adddinin Kiristanci,inda suka kuduri aniyar basu dama kuma a’a duba da sakamakon da suka samu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan