Home / Jirwaye / Kwankwaso Ba Zai Sake Tasiri Ba A Siyasar Kano – Inji Wani Kwamishina

Kwankwaso Ba Zai Sake Tasiri Ba A Siyasar Kano – Inji Wani Kwamishina

Shugaban kwamitin hulda da jama’a na kungiyar yakin zaben Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, Malam Muhammad Garba, ya ce ya bayyana dalilin da ya sa tsohon gwamnan jihar, Rabiu Musa Kwankwaso ya ki sake tsayawa takarar sanata inda ya ce tsohon gwamnan yana tsoron tsohon gwamna Shekarau ne ya sanya hakan

Garba wanda shine kwamishian yada labarai na jihar Kano, ya bayyana hakan ne a yayin da ake gudanar da yakin neman zaben gwamnan jihar Kano a karamar hukumar Karaye a jihar Kano. Inda ya bayyana cewa a yanzu Kwankwaso ba shi da wani tasiri a siyasance.”

Yace “Sanata Kwankwaso ya karanta rubutun da ke bisa kan bango kawai ya ja da baya, saboda yana tsoron kada a wulakanta shi a ranar zabe don zai kara da tsohon gwamnan jihar Kano Mal. Ibrahim Shekarau, Sardaunan Kano.

“Idan za ku iya tunawa Shekarau a 2003 zuwa 2007 ya lallasa Kwankwaso a lokacin takarar gwamna sannan kuma ya kada dan takarar gwamnansa a shekarar 2007. “Kalamun Kwankwaso suna nuna cewa ya san ba shi da wani tasiri kuma a harkar siyasar jihar Kano,” inji shi.

Garba ya ce “kungiyar Kwankwassiya tare da sauya shekar da mafi yawancin jiga-jigan kungiyar zuwa jam’iyyar APC ya nuna cewa tsohon gwamnan tare da dan takararsa na gwamna sun gama faduwa kafin ma a gudanar da zaben.”

About Labarai24

Wannan Jarida ce ta shafin Intanet dake kawo muku labarai da rahotannin. har da Bidiyo da Audio.

Check Also

Rugujewar Kwankwasiyya ta kunno kai a jihar Kano – Fa’izu Alfindiki

Fitaccen mai adawa da tsarin siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso kuma …

One comment

  1. Could you inform me what style are you utilizing on your web site?

    It looks good.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *