Wata Sabuwa: Buhari ba cikakken Bafulatani ba ne- Atiku

133
Atiku da sauran jiga-jigan PDP

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ce Buhari ba cikakken Bafulatani ba ne saboda ba zai iya yin magana da Fulatanci ba.
Atiku ya bayyana haka ne ranar Litinin a jihar Jigawa lokacin gangamin yakin neman zabe.

Atiku, wanda ya bayyana Buhari a matsayin Bafulatanin bogi, ya ce: “Bafulatanin asali ba zai ja mabiyansa zuwa matsanancin talauci ba kamar abinda yake faruwa a gwamnatin APC”.

Atiku ya je jihar Jigawa ne don samun goyon baya daga masu zabe don kada Buhari.

Ya yi alkawarin gudanar da ayyuka uku a jihar ta Jigawa idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a zaben wata mai kamawa.

Ya ce ayyukan, kamar yadda tsohon gwamna, Sule Lamido ya bukata sun ne fadada Kogin Hadeja, gina hanyar Gaya-jahun zuwa Kafin Hausa da kuma ginin hanyar Kwanar Dumawa zuwa Babura.

A jawabinsa, tsohon gwamna Sule Lamido ya roki masu zabe a jihar Jigawa da su zabi Atiku, yana mai cewa zaben 2019 zabe ne “tsakanin cancancta da rashin cancancta, tsakanin dan takarar gangarriya da jama’a ke so da dan takarar bogi”.

Haka kuma a taron yakin neman zaben, shugaban jam’iyyar PDPn na kasa, Uche Secondus ya gargadi Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC da kada ta kuskura ta yi wani yunkurin yin magudin zabe.

Haka shi ma ya yi kira ga masu zabe a jihar ta Jigawa da su zabi dan takarar jam’iyyar.

“Dandazon dake taruwa a wajen yakin neman zabenmu abu ne mai kayatarwa, shi yasa muke gargadin INEC da kada ta kuskura ta yi yunkurin juya zaben shekarar nan”, in ji Uche.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan