Abinda yasa aka kore ni daga TETFUND- Dakta Bichi

170
Dakta Abdullahi Baffa Bichi

Tsohon Babban Sakataren Asusun Tallafawa Manyan Makarantu, Dakta Abdullahi Baffa Bichi ya ce an kore shi daga ofis ne sakamakon kin ba Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu cin hanci.

Jaridar Kano Today ta bada rahoton cewa a ranar Litinin ne Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ya maye gurbin Dakta Baffa Bichi da tsohon Babban Sakataren TETFUND din, Sulaiman Bogoro ba tare da bada wani dalili ba.

“Ina so in tabbatar muku da cewa ban taba karbar ko ficika ba daga kowace makaranta. Idan an samu wata hujja a kaina, a shirye nake in karbi hukuncin kisa”, in ji Dakta Bichi.

Amma tsohon Babban Sakataren TETFUND din ya fada wa tashar BBC Hausa cewa Ministan ya turo wani dan kwangila yana bukatar a ba shi rabonsa daga Naira Biliyan 200 da TETFUND din ya raba wa makarantu.

“Ko da a ce na rika karbar kaso 10 cikin dari daga kowace makaranta, da na lankwame a kalla Naira Biliyan 20.

“Ina so in tabbatar muku cewa ban taba karbar ko ficika ba daga kowace makaranta, idan an samu hujja a kaina, a shirye nake in karbi hukuncin kisa”, a kalaman tsohon Sakataren.

Dakta Bichi ya ce Ministan ya zarge shi da rashin bada damar haduwa da shi, rashin biyayya da kuma yin magana da manema labarai ba tare da izini ba.

Yayinda yake musanta dukkan zarge-zargen, Dakta Bichi ya ce ya fi zama a Ma’aikatar Ilimi fiye da TETFUND, saboda ya ya rika yin aiki a matsayin mataimaki.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan