Ezekwesili ta janye daga takarar shugaban kasa

170
Dakta Oby Ezekwesili

A ranar Alhamis din nan ne Dakta Oby Ezekwesili, ‘yar takarar shugaban kasa a jam’iyyar ACPN ta janye daga takarar shugaban kasa don bada damar kulla wani kawance mai karfi da zai iya kayar da jam’iyyun APC da PDP a zaben 16 ga watan Fabrairu, 2019.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Kwamitin Yakin Neman Zaben Takarar Shugaban Kasa na Ezekwesili, Ozioma Obabukoh ya fitar, an jiyo Ezekwesilin tana cewa yanke hukuncinta na janye wa daga takarar shugaban kasar ya biyo bayan tattanawa mai zurfi da ‘yan Najeriya a gida da waje.

A cewarta, lura da yanayi siyasar da kasar nan ta shiga kafin Muhawar ‘Yan Takarar Shugaban Kasar da da aka shirya gudanarwa ranar 19 ga watan Janairun nan shi ya kara gaggauto da yanke hukuncin.

Sanarwar ta ce: “Wannan mataki ya biyo bayan zazzafar tattaunawa da shugabanni daga dukkan sassan rayuwa a kasar nan a ‘yan kwanaki kadan da suka gabata. Na fahimci ya zama wajibi a gare ni da in mayar da hankali wajen taimakawa a gina wani kawance mai karfi don tabbatar da wani zabi mai kyau ga PDP da APC a zabuka masu zuwa”.

“Na yarda sosai cewa wannan kawance mai fadi don samun wani zabe mafi kyau ya fi irin na baya, wani aiki na gaggawa don kuma a madadin ‘yan Najeriya. Saboda haka, na zabi in jagoranci kishin kasa irin wanda aka fi bukata don farfado da kuma yi wa kasarmu saiti”, in ji Misis Ezekwesili.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan