Tarihin Shugabannin Ƴan sandan Najeriya tun daga Farko zuwa Yau (1)

488

Rundunar Yansanda ta kasa (NPF) hukuma ce da take dauke da nauyin kare hakkin rayuwa da dukiyar al’ummar kasa. Hukumar tana da rassa a jihohin kasar nan tare da manyan shiyyoyi 12.

An kafa rundunar ne a shekarar 1820, ta samu sauye-sauye musamman a tsarin gudanarwa masu yawan gasket un daga kafa ta kawo yanzu.

A shekarar 1960 ne aka hade bangarorin hukumar inda aka mayar da hukumar cikakkiyar rundunar yansanda ta kasa.

Ga jerin takaitaccen Tarihin wadanda suka shugabanci hukumar

LOUIS EDET:

Ya kasance shi ne dan kasa na farko da ya rike mukamin shugabancin Rundunar ‘Yansanda. An haife shi a garin Calabar dake jihar Cross River a shekarar 1914. Ya koma ga mahalliccinsa a shekarar 1979.

Ya kasance mutum mai kwazo tare da kishin kasa. Ya rike mukamin shugaban rundunar yansanda ta kasa daga shekarar 1964 zuwa 1966. A lokacin da yake raye, ya rike mukamin shugaban kungiyar kwallon kafa ta kasa na wucin gadi (briefly) a shekara na 1960.

KAM SELEM:

Shi ne shugaban Rundunar yansanda na biyu. A shekarar 1966. Mr Kam Selem ya karbi ragamar mulki daga hannu Mr Louis Edet. Ya kasance shugaban hukumar yan sanda ta kasa daga shekarar 1966 zuwa shekarar 1975.

A yayin da yake shugabanci, ya fuskanci kalubale da dama wanda suka hadar da; kisan gillan da akayi wa Sir Abubakar Tafawa Balewa tare da sauran manyan kasa a shekarar 1966. Ya kuma fuskanci matsin lamba daga hannun yan jarida bisa zargin da suke yi gwamnatin general Yakubu Gawon da gudanar da almundahana da dukiyar al’umma.

ALHAJI MUHAMMADU DIKKO YUSUF:

Shi ne shugaban Rundunar Yansanda na uku. An fi sanin shi da sunan MD YUSUF. Ya jagoranci rundunar daga shekarar 1975 zuwa 1979 a zamanin mulkin Gen Murtala Muhammad da Gen Olusegun Obasanjo.

Bayan aikin Dansanda, MD YUSUF ya shugabanci Grassroot Democratic Movement, jam’iyar siyasa ta kasa a lokacin dawo da ragamar mulkin kasa zuwa hannun farar hula wanda Gen. Sani Abacha ya kaddamar a shekarar 1997 zuwa 1999. Ya samu mukamin chairman na Arewa consultative forum a shekarar 2000, kungiyar Arewacin kasar nan ta siyasa da al’adu.

MALAM ADAMU SULAIMAN:
Shi ne shugaban Rundunar Yansanda na hudu. Ya karbi shugabanci daga hannun MD YUSUF. Kuma ya shugabanci hukumar daga shekara ta 1979 zuwa 1981. An haife shi a garin Jimeta, jihar Adamawa a ranar 14 ga watan May shekarar ta 1929.
Yayi makarantar Jimeta Elementary School da Yola Middle School da Barewa Collage Zaria daga shekarun 1940 zuwa 1950.

Daga nan sai ya tafi Collage of Technology Zaria. Bayan ya kammala, ya sami gurbin karatu kai tsaye a Jami’ar Ibadan kuma ya samu sakamako mai kyau. A shekarar 1916 ya sami shiga rundunar Yansanda ta kasa. A shekarar 1966 ya samu mukamin shugaban Rundunar, karkashin shugabanci Shehu Shagari.

MR. SUNDAY ADEDAYO ADEWUSE: Shi ne shugaban Rundunar yansanda na biyar. Ya gaji Mal. Adamu Sulaiman, ya rike ragamar mulki Rundunar daga shekara ta 1981 zuwa 1983.

An haife shi a rananr 6 ga watan December a shekara ta 1936 a garin ogbomoso dake jihar Ogun. Ya fara karatu a Mada Station daga nan ya wuce Baptist Day school a garin Jos a shekarar 1944 zuwa 1950.

Yayi makarantar secondary a garin Keffi. Ya samu shiga rundunar Yansanda a shekarar 1957. Ya samu damar Karin karatu a police staff collage a Scotland da East Ridding Constabulary, Landshire, Yorkshire. Ya rasu a ranar 26 ga watan January shekara ta 2016.

ETIM OKON INYANG: Shi ne shugaban Rundunar Yansanda na shida Ya karbi shugabanci a shekarar 1983 zuwa shekarar 1986. An haife shi a ranar 26 ga watan December shekarar 1931 a garin Enwang-Oron, jihar Akwa Ibom. Yayi karatu a makarantun Roman catholic school, Uko-Akpan, Methodist school, Oron da kuma Oyubiya secondary school Oron daga shekarun 1936 zuwa 1945.

Ya samu shiga rundunar Yansanda ta kasa a shekarar 1949. Kafin shigarsa rundunar, ya kasance malami a shekarun 1946 zuwa 1949. Ya samu shiga rundunar Yansanda ta kasa a matsayin constable, daga bisani yayi ta samun karin girma har ya kai ga matsayin shugaban rundunar. Ya rasu a ranar 26 ga watan September shekarar 2016.

MAL MUHAMMAD GAMBO JIMETA:

Shi ne shugaban Rundunar yansanda na bakwai. An haife shi a garin jimeta, jihar adamawa. An nada shi shugabancin rundunar a shekara ta 1986 zuwa 1989. Baya ga haka, ya kasance mai bada shawara ga shugaban kasa akan harkokin tsaro, a lokacin mulkin shugaban kasa GEN. Ibrahim Babangida.

MAL ALIYU ATTA:

Shi ne shugaban Rundunar yansandar na takwas. Ya karbi ragamar mulki daga shekara 1989 zuwa 1983. An haife shi a jihar Adamawa.

ALHAJI IBRAHIM COOMASSIE:

Shi ne shugaban Rundunar yansanda na tara. An haife shi a ranar 18 ga watan march shekarar 1942 a jihar Katsina. Ya rike mukamin shugaban rundunar yansanda ta kasa daga shekarar 1993 zuwa 1999, karkashin mulkin soja na GEN. Sani abacha da Gen. Abdussalam Abubakar.

Yayi karatu a makarantun Provincial Secondary School Zaria, Barewa Collage Zaria, Detective Collage, Wakefield, UK da kuma Washington DC a kasar Amurka. Mal Ibrahim ya gudanar da bincike da dama wanda suka hadar bincike akan mutuwar M.K.O Abiola, da bincike akan mulkin Gen. Babangida, da bincike akan mutuwar tsohon shugaban kasa Gen Sani Abacha.

Bayan yayi ritaya daga aikin dan Sanda, ya zama member a kungiyar Jama’atul Nasrul Islam na jihar Katsina, haka nan, yana daga cikin (Board of Trustees) na Arewa Consultative Forun na jihar Katsina. Ya kasance mai gudanar da ayyukan raya kasa har zuwa karshen rayuwarsa. Ya rasu a ranar 19 ga watan July, shekarar 2018.

Ku biyo mu a rubutu na gaba don jin cigaban ragowar shugabannin rundunar ta ‘yansandan Najeriya…

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan