Tata ɓurza: Jam’iyyar Ezekwesili za ta marawa Buhari baya

159
Tambarin jam'iyyar ACPN

Jam’iyyar ACPN, jam’iyyar da Dakta Oby Ezekwesili ta janye daga takarar shugaban kasa ta ce za ta mara wa Shugaba Muhammadu Buhari baya a zaben shugaban kasa na ranar 16 ga watan Fabrairu, 2019.

Wannan ci gaban dai ya zo ne sa’o’i kadan bayan da Dakta Oby Ezekwesili, ‘yar takarar shugaban kasa a jam’iyyar ta janye daga takarar.

Da yake yi wa manema labarai jawabi, shugaban jam’iyyar na Kasa, Sani Galadima ya ce Dakta Ezekwesili ta so ta yi amfani da doron jam’iyyar ne kawai don samun mukamin Ministar Kudi, yana mai karawa da cewa tsohuwar Ministar Kudin ba ta nuna alamar yi da gaske ba a yakin neman zaben nata.

Dakta Oby Ezekwesili

“Dalilin kiran wannan taron manema labarai shi ne a sanar da duniya game da gurin zama shugaban kasa na Dakta Oby Ezekwesili, wanda a zahirin gaskiya ba gaskiya ba ne. Daya daga cikin mataimakanta, Iyinoluwa Aboyeji ya ba ni tabbacin cewa kawai ta so ne ta yi amfani da doron jam’iyyar ACPN don tattaunawa kan yadda za ta zama Ministar Kudi ta Najeriya.

“Ba ta ga cewa ya kamata ta sanar da jam’iyyar da take rike da tutarta wannan bukata tata ba. Idan kun lura, Dakta Oby Ezekwesili ita kadai ce ‘yar takarar da take da tsageranci sosai a yakin neman zabenta ba tare da wani kwakkwaran abu a kasa ba da zai nuna cewa da gaske take a yakin neman zaben nata.

“Babu sakatariyar yakin neman zabe, babu allon talla ko wata babbar alama da za ta nuna cewa da gaske take. Bisa wannan dalilin ne jam’iyyar ACPN take janye goyon bayanta daga gurinta na takarar shugaban kasa za ta kuma mara wa gurin zama shugaban kasa a wa’adi na biyu na Shugaba Muhammadu Buhari baya don daukar Najeriya zuwa mataki na gaba”, a kalaman Mista Galadima.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan