Wata Mata Ta Maka Mijinta A Kotu Saboda Ya Tura ‘Ya’yansu Almajiranci

218

Wata mata mai suna Jamila Abubakar ta maka tsohon mijin ta Isah Aliyu a kotu dake magajin Gari, Kaduna saboda tura ‘ya’yan su makarantar Allo da yin bara da yayi a wani kauye kusa da su.

Isah dai ya saki Jamila ne kimanin watanni uku kenan. Sannan kuma bayan haka sai ya tattara ‘ya’yan su ya tura su makarantar Allo a wani kauye.

Jamila ta roki Kotu da ta tilastawa tsohon mijin na ta da ya dawo da wadannan yara cikin gari inda suke makarantar Boko da Islamiyya.

A na sa jawabin a gaban Alkali, Isah ya karyata wannan zargi da matar sa ta yi ya ce dalilin da ya sa ya saki matar sa shi ne domin taki bin sa kauyen da yake da zama.

A karshe Alkali ya yanke hukuncin tabbatar da saki a tsakanin su sannan ya umarci Isah ya taho kotu da wadannan yara nan da mako guda.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan