Zan Dawowa Da Ƙasar Nan Matsayinta A Fannin Tattalin Arziƙi – In Ji Atiku

51

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma ɗan takarar kujerar shugaban ƙasa a tutar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya lashi takobin dawowa da ƙasar nan martabarta ta mafi kyawun tattalin arziki a nahiyyar Afirka.

Atiku Abubakar ya sha alwashin habaka tattalin arzikin ƙasar nan ta fuskar dawo da martabar hannayen jari na ‘yan kasuwannin kasashen ketare da a baya ta yiwa sauran kasashen nahiyyar Afirka fintinkau.

Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba. Ya kumq bayyana takaicin sa game da damuwa dangane da yadda ƙasar Ghana ta sha gaban ƙasar nan ta fuskar tattalin arziki a nahiyyar Afirka.

Idan za’a iya tunawa a cikin makon nan ne sashen masana’antu da kuma cigaba na majalisar ɗinkin duniya ya fitar da sakamakon bincike akan kasashe mafi kyawun tattalin arziki.

Sakamakon binciken majalisar ya bayyana yadda ƙasar nan ta zamto koma baya a sakamakon yadda masu hannun jari na kasashen ketare ke ficewa daga harkokin kasuwanci na kasar nan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan