Ƙungiyar Dattawan Igbo Ta Buƙaci A Zaɓi Atiku

198

Ƙngiyar dattawan kabilar Igbo da ke kudu maso gabashin ƙasar nan, Ohaneze Ndigbo, ta yi kira ga dukkan ‘yan kasar su zabi dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, a zaben 2019.

Tun da farko dai tsohon mataimakin shugaban kasar ya zabi Peter Obi, dan kabilar Igbo kuma tsohon gwamnan jihar Anambra, a matsayin mataimakinsa.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ranar Alhamis, ta ambato shugabanta, Mr John Nwodo, na cewa sun ɗauki matakin ne bayan majalisar kolin Ohaneze Ndigbo ta tattauna a Enugu kan ɗan takarar da ya kamata su mara wa baya a zaben watan Fabrairu.

“A kokarinta na ganin an gudanar da siyasa mai tsafta, majalisar koli ta Ime Obi Ohaneze Ndi Igbo ta gana ranar Alhamis 24 ga watan Janairun 2019 kan makomar kasarmu. Bayan ta yi azari sosai kan manufofin kowanne dan takara musamman kan batun sake tsarin kasar nan da kuma bai wa yankin kudu maso gabas muhimmanci, Ohaneze ta ji dadin yadda PDP ta zabi danta Peter Obi a matsayin mataimakin shugaban kasa.

“Domin haka take ganin dan takarar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ne ya dace ta mara wa baya saboda alwashin da ya sha na sake fasalin kasar nan, kuma ya jaddada hakan lokacin ziyarar da ya kai Amurka kwanan baya.”

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan