Baƙaƙen Maganganu 16 da Obasanjo ya Faɗawa Atiku amma yayi Amai ya Lashe

192

Bayan rasuwar tsohon shugaban kasa Gen Sani Abacha, shugaban ru(ƙon kwarya na wancan lokaci watau Gen Abdussalam Abubakar yayi bakin kokarinsa domin ganin an mika ragamar mulki zuwa hannun farar hula.

Bayan gudanar da zaben, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da mataimakinsa Atiku Abubakar ne suka lashe zabe.
A yayin da suke gudanar da mulki, sai rashin jituwa ta auku a tsakanin su, sanadiyyar hakan shugaba Obasanjo ya furta wasu kalamai akan mataimakin nasa. Daga wannan lokaci zuwa yanzu, tsohon shugaban yayi kalamai da dama akan tsohon mataimakin nasa kuma dan takarar shugabancin kasa yanzu a karkashin jam’iyyar PDP a zaben 2019.

Atiku Abubakar

Ga irin abubuwan da tsohon shugaban ya fadi akan Alhaji Atiku Abubakar.

A shekarar 2003, “Nayi nadamar zaben Atiku Abubakar a matsayin mataimaki na”.
A shekarar 2004, “Ba zan iya aiki tare da Atiku Abubakar ba saboda ban aminta da gaskiya da rukon amanarsa ba”.
A shekarar 2005, “ Atiku ba mutum ne da za’a amincewa ba”.
A shekarar 2006, “ Atiku ba zai iya gujewa shari’a ba bisa zarge-zargen cin hanci da rashawa”.
A shekarar 2007, “ karku zabi Atiku, shi shugaba ne mai handama da babakere”.
A shekarar 2008, “ Atiku azzalumin shugaba ne”.
A shekarar 2009, “ Ƴan Najeriya ba zasu taba yafe wa Atiku ba”.
A shekarar 2010, “ Atiku baya daga cikin zabin da ya dace da shugabancin kasar nan”.
A shekarar 2011, “Ban taba ganin shugaba mai hadama kamar Atiku ba”.
A shekarar 2012, “Ya kamata yan Najeriya suyi addu’ar samun shugabanni masu gaskiya da rukon amana”.
A shekarar 2013, “Ya kamata Atiku ya bawa yan Najeriya hakuri bisa laifukan da ya aikata a siyasance.
A shekarar 2014, “Babu wata jam’iyyar siyasa da take da burin karbar shugabanci da zata yi tunanin Atiku”.
A shekarar 2015, “Ƙasarnan tafi karfin azzalumin shugaba kamar Atiku”.
A shekarar 2016, “Ba zan taba shiryawa da Atiku ba”.
A shekarar 2017, “Ban taba sanin cewa Atiku ya gurbace haka ba, ba zamu taba jituwa ni da shi ba. Allah ya tsare ni”.
A shekarar 2018, watan Janairu, “ Allah ba zai yafe min ba idan na goyi bayan Atiku”.

Bisa irin kalaman da tsohon shugaban kasa Obasanjo yayi akan tsohon mataimakin nasa, shin kuna ganin ya dace ya karbi mulki daga hannun shugaba Muhammadu Buhari?

A shekarar 2018, watan August, “Atiku yana da kwazon da zai iya ceto kasar nan daga yanayin tabarbarewan tattalin arzikin da ta shiga” Bugu da kari, wani irin kallo zaku yi wa dattijo Obasanjo, domin kuwa Hausawa sunce idan mafadin magana wawane, To mjiyinta ba wawa bane.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan