Jam’iyyar APC a jihar Zamfara ta bijire wa umarnin Hukumar Zabe

167
Tambarin jam'iyyar APC

Jam’iyyar APC Reshen Jihar Zatmfara ta bijire wa umarnin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC inda ta saki sunayen mambobin kwamitocinta na yakin neman zabe gabanin zabukan 16 ga watan Fabrairu da 2 ga watan Maris, 2019.

Za dai a iya tuna cewa Hukumar ta INEC ta nace kan cewa jam’iyyar ta APC a jihar Zamfara ba ta da dan takara ko daya sakamakon korafe-korafe da suka dabaibaye zabukan fitar da gwanin da jam’iyyar ta yi ikirarin ta yi.

Shugaban jam’iyyar na jihar, Lawal Liman ya sanar da haka ga manema labarai a Gusau ranar Talata.

To sai dai a ranar Juma’a da ta gabata, Babbar Kotun Jihar Zamfara mai Lamba 3 dake zamanta a Gusau, wadda Mai Shari’a Bello Shinkafi ke jagoranta ta tabbatar da zaɓukan fitar da gwanin da jam’iyyar ta yi a ƙarƙashin shugabancin Lawal Liman.

Haka kuma, Kotun ta roƙi Hukumar ta INEC da ta karɓi sunayen ‘yan takarar da zaɓukan fitar da gwanin ya samar.

Shugaban Jam’iyyar, Lawal Liman ya ce kwamitocin sn hada da Babban Kwamiti, wanda ya kunshi mambobi 60 karkashin jagorancin Shugaban Ma’aikatan Gwamna Abdul’aziz Yari, Abdullahi Abdulkarim. Sakataren jam’iyyar APC na jihar, Sani Musa zai zama Sakataren wannan kwamiti.

Shugaban Jam’iyyar ya kara da cewa akwai kuma kwamitocin kananan hukumomi wadanda suka kunshi mambobi 518.

A cewar Shugaban Jam’iyyar, a kowace ƙaramar hukuma a cikin ƙananan hukumomi 14 dake jihar, kwai mambobi 37 da jam’iyyar ta bayar da sunayensu waɗanda za su kula da harkokin yaƙin neman zaɓe a yankunansu daban-daban.

Ya ci gaba da cewa jam’iyyar ta kuma nada Gwamna Abdul’aziz Yari a matsayin Shugaban Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na Jam’iyyar APC a jihar.

Ya ce shi wannan kwamiti yana da mambobi 111, kuma Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Abdullahi Shinkafi ne Sakataren Kwamitin.

Shugaban Jam’iyyar ya bayyana jin dadinsa ga mambobin jam’iyyar APC a jihar sakamakon hadin kai da suke ba shugabancin jam’iyyar.

Ya roke su da su ci gaba da ba jam’iyyar hadin kai don samar da ayyukan ci gaba masu ma’ana a jihar da kasa baki daya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan