Onnoghen: Lauyoyi sun yi watsi da umarnin NBA na ƙaurace wa kotuna

152
Mai Shari'a Samuel Walter Onnoghen

Lauyoyi sun yi watsi da umarnin da Kungiyar Lauyoyi ta Kasa, NBA ta ba su na su kaurace wa kotuna a wani mataki na nuna fushi da dakatar da Babban Alkalin Najeriya, Samuel Walter Onnoghen da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi.

An ci gaba da sauraren shari’u a yau a Kotun Koli ta Kasa, wadda Mai Shari’a Mary Peter Odili ke jagoranta.

Dakatar da Mai Shari’a Samuel Walter Onnoghen dai ya jawo ka-ce-na-ce a kasar nan, inda wasu suke ganin matakin yana bisa doka, wasu kuwa suna ganin akasin haka.

An dakatar da shi ne sakamakon kin bayyana kadarorinsa da kuma badakalar cin hanci.

Fadar shugaban Kasa ta ce ta bi umarnin Kotun Da’ar Ma’aikata ne, CCT wajen dakatar da Babban Alkalin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan