Ƙarni na (21) Karni ne da yake da tarin ci gaba a zamantakewa, duba da yadda sauyin zamantakewar dan adam take samun cigaba ta fanni daban-daban. Ganin haka kowa yake kokarin samun ilimi a wannan karni, maza suna kokarin neman ilimi, haka matan da ba Hausawa ba suma suna wannan kokarin da maza suke na neman ilimi. A iya nazarina na kalli zamantakewar mutanan kasar Hausa dake a Arewacin Najeriya da tsarin zamantakewar matan Hausawa ganin yadda muke samun karuwar yawan Al’umma, duba da yadda ake samun yawaitar mata a wannan lokacin.
Mata ne suka fi kowa yawan larura a cikin kowacce Al’umma, matan Hausawa kuma sune koma baya wajan zuwa makaranta, in muka kalli Nigeriya da kyau, kasace mai tasowa da karfin yawan al’umma (Population), in muka hada ta da kasashe masu karfin tatallin arziki a duniya (advance economy countries), zamuga cewa yawansu yana anfanar dasu, duba da yadda mata da maza suke kokarin neman ilimi da kokarin samun madafin iko kama daga aikin Gwamnati da shiga harkokin da suka shafi al’umma da yin aiki tukuru dan tsira. Bincike ya tabbatar da Nigeriya tana da yara mata sama da 6.9 million wanda basa cikin karamar makaranta (primary school), da matan da basu da ilimi gaba daya wanda ko yaushe yawansu yana karuwa, wannan ba karamar matsala bace a zamantakewar dan adam.
Muna ganin mace tayi aure shine abinda yafi mata sauki, ba sai ta sami ilimi ba duba da akwai wanda ake ciresu daga makaranta ana musu aure saboda yanayin girman jikinsu ko, balagarsu (purvarty), duk wannan yana faruwa ne a kasar Hausa.
In muka kalli yadda mata suke zama abin tausayi lokacin da suke zuwa wajan da ilimi ne yake aiki, suna cizan yatsa wanda mata ne ya kamata ka gani a wajan sai kaga maza ne, ko matan da ba Hausawa ba wannan shine misali da yake fitowa kururu wanda mace in taje asibiti (hospital), tana boye rashin lafiyar da yake damun ta duba da yadda ta sami yanayin asibitin da taje ganin wanda zai dubata ba mace bace yar’uwarta na miji ne, wanda zataji kunya na bayyana masa rashin lafiyarta na matantakarta (Gynecology), ko kuma ta sami macen da ba yaransu daya ba wanda ita batajin yaranta itama batajin yaranta, mun sami koma baya tanan Fanni rashin bawa mace dama tayi ilimi a karni na (21), beyi rana ba.
Kasa tana samun koma baya ta fannin tattalin arziki (economic depression), na rashin ilimin mata domin kuwa suma suna da nasu tunanin da basira da zasu iya kawo nasara da dorewar kasa mai karfin tattalin arziki, a lokacin da suka sami ilimi.
haka yasa yankin arewa (northern Nigeria), ya zama koma baya domin matan suna zama abin tausayi a kusa da karshen rayiwarsu, wani nazari mai zurfi da nayi akan rasuwa da yawan al’umma (mortality and population), na gano cewa maza ne suke mutuwa da wuri akan mata, kuma mata sun fi maza yawa. Wannan yasa na Kalli matan da suka rasa mazan su kuma basu sami dama ta gina kansu ba ta fannin ilimi.
Wannan binciken ya tabbatar da suna shiga hali mai tsanani, domin kuwa mace idan ta tashi babu ilimi, mijin da yake aurenta idan ya rasu, ga yara kuma masu tasowa da wanne zata ji, neman abinda zasu kai bakinsu, ko karatun Su, gashi kuma bata da aiki bata da sana’a tayaya zata sami damar kula da kanta da sauran yaranta, ga tai mako kuma yanzu yana nema ya gagara.
Ya zama wajibi akanta ta fita tayi aikin wahala domin samu su tsira da cikin su. Yara kuma daga lokacin da basa samun abinci sau uku a rana dole su fita su nemi abinci ta ko wacce hanya, ko mace ko na miji. Wannan wata gaba ce da zanyi rubutu na musanman a kai nan gaba kadan.
Rashin ilimin mata ne yasa ake zubar da yara akan hanya, ko suke yawan tallace-tallace wanda da yawa masu gurbataccen tunani suke zagi da kyamatar matan da suke zuwa makaranta, suka zubawa masu talla ido domin suna siyan Goro da Dan wake a wajansu, ma’ana suna samin biyan bukata lokacin da suke zaune, za a kawo musu su siya, na miji kuma yana da sha’awa, mace ma haka ga talauci kuma yana sa a sai da mutunci. Zaiyi wahala kaje kotu (Court), ko gidan yari (prison), ko chaji ofishin yan sanda (police station). Kaga ana chajin mace yar boko da wani laifi.
Wanda ya sabawa Allah ko tsarin mulkin Nigeria (Constitution), ko ba komai ilimi ya zama fitila mai yaye duhu ga rayuwar dan adam a zamantakewa.
Meyasa matan da basu da ilimi ne kawai ake safararsu zuwa kasashe waje (women trafficking), meyasa matan da basu da ilimi ne suke yawo da yaransu akan titi suna barar abinda zasuci? meyasa matan da basu da ilimi ne suke zama a gidan mata masu zaman kansu? meyasa matan da basu da ilimi ne suke yawan mutuwa lokacin haihuwa (maternal mortality) meyasa bazamu bar mata suyi ilimi ba domin samun al’umma ta gari. Tambayar da zamu bawa kanmu amsa kenan.
Daga
Shuaibu Lawan.
shuaibu37@gmail.com
08037340560 Saƙo Kawai (Text Only)
Miyasa yawancin mata sukafi maza tsowon rai aduniyane.