Kotu ta yi watsi da ƙarar Onnoghen

159
Samuel Walter Onnoghen

Kotun Daukaka Kara ta Najeriya ta yi watsi da karar da tsohon Alkalin Alkalan Najeriya, Walter Onnoghen ya shigar, inda yake bukatar kotun ta hana Kotun Da’ar Ma’aikata, CCT sauraron karar da Gwamnatin Tarayya ta shigar da shi.

A cewar BBC, kotun ta yanke hukuncin ne ranar Laraba, kuma ta yi watsi da bukatar ne saboda ba a gabatar da dalilan sauraron karar ba kamar yadda dokokin shari’a suka tanada.

BBC ta kara da cewa hukuncin na nufin Alkalin Alkalan zai ci gaba da fuskantar tuhuma a gaban Kotun Da’ar Ma’aikatan, wadda ta dage zamanta domin dakon sakamakon karar da Mr Onnoghen ya daukaka.

Shugaba Buhari ne ya dakatar da Mista Onnoghen bisa shawarar Kotun Da’ar Ma’aikata wadda ta samu Alkalin Alkalan da laifin kin bayyana cikakkun kadarorinsa lokacin da aka nada shi mukamin Alkalin Alkalai a shekara ta 2017, kamar yadda majiyar BBC Hausa ta tabbatar.

Amma Mista Onnoghen ya ce ba da gangan ya yi hakan ba, ya ce mantawa ya yi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan