‘Yan bindiga sun sace Sakataren Watsa Labaran Gwamnan jihar Taraba

43
Gwamna Darius Ishaku na Jihar Taraba

‘Yan bindiga sun sace Hassan Mijimyawa, Sakataren Watsa Labarai na Gwamnan Jihar Taraba, Darius Ishaku.

A yau da sassafe ne ‘yan bindigar da ba a san ko su wane ne ba suka sace Mista Mijimyawa a hanyar Bali zuwa Gashaka.

Wata majiya da ta yi magana da jaridar Tribune Online ta kuma bukaci a sakaya sunanta ta ce an sace Sakataren ne lokacin da yake tafiya a cikin motarsa ta aiki.

“Yau aka sace shi yayinda yake kan hanyar zuwa ganin Gwamna wanda ya yi tafiya jiya zuwa Gashaka don wani aiki, Sakataren Watsa Labaran bai kamata ya yi tafiyar ba, amma akwai wasu abubuwa da Gwamnan ya bari, wadanda ake bukatar su cikin gaggawa a Gashaka yau.

“A yau da sassafe ya tafi da direbansa, kawai sai muka ji cewa matarsa ta kira Mataimakin Gwamnan Jihar Taraba, Haruna Manu cewa an sace mijinta.

“A cewar uwar gidan, ‘yan bindigar sun tare motar ne, suka fito da Sakataren Watsa Labaran shi kadai, suka kyale direban, ‘yan bindigar daga bisani sai suka yi amfani da wayar Sakataren Watsa Labaran suka kira matarsa”, a cewar majiyar.

Mataimakin Gwamna Jihar Taraba, Mista Manu ya tabbatar da sace Sakataren Watsa Labaran ga manema labarai a waya, ya ce uwar gidansa ta zo gidansa don sanar da shi sace mijin nata.

“Yanzun nan matar Sakataren Watsa Labaran ta bar gidana, ta fada min cewa bisa bayanan da ake da su, masu garkuwa da mutanen suna da yawa, suna rike da bindigogi kirar AK47, ta ce suka fito da mijinta suka kyale direban, masu garkuwa da mutanen kuma sai suka kira ta da wayar mijin nata.

“Kada mutanen jihar nan su tayar da hankulansu, wannan lokaci ne da ya kamata mu yi addu’a ga Hassan da kuma jihar nan, mutumin da ya bar gidansa da sassafen nan a yanzu yana hannun mugaye, abin damuwa ne babba”, in ji Mista Manu.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Taraba, David Akinlemi wanda ya ce an kira shi game da al’amarin ya ce ba zai iya tabbatar da al’amarin ba har lokacin da aka rubuta wannan rahoto.

“An kira ni game da al’amarin amma ba zan iya fada muku ainihin abinda ya faru ba. Na tura jami’anmu zuwa wajen har sai na samu cikakken bayani daga jami’anmu”, in ji Mista Akinlemi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan