Abinda yasa ban taba kyale Atiku ya zama Muƙaddashin Shugaban Ƙasa ba-Obasanjo

139
Cif Olusegun Obasanjo

Tsohon Shugaban Kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana dalilan da yasa bai taba ayyana tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ba a matsayin Mukaddashin Shugaban Kasa a lokacin da suka yi mulki.

Ya ce bai tattara iko ga Atiku ba saboda ba shi da bukatar ya yi tafiya ya bar kasar nan har na tsawon kwanaki 104 kamar yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya yi lokacin da ya tafi Landan don duba lafiyarsa.

Mista Obasanjo, wanda ya bayyana haka a yayin da yake gabatar da wata makala a Wani Taron Jawabin Kasuwanci da Ake Gabatarwa Duk Bayan Wata Uku a Jihar Legas, ya bayyana cewa kuskure ne yadda wasu jama’a ke cewa ya takure mataimakinsa a lokacin mulkinsu.

A cewasa, Babu Wani Shugaba Mai Cikakken Iko da aka taba yi a Najeriya da ya bada dama ga mataimakinsa kamar yadda ya ba Atiku.

“Atiku ya jagoranci wasu abubuwa a wasu ‘yan lokuta da na bar kasar nan don wani aiki. A irin wadancan lokatai, ya jagoranci Tarukan Ganawar Majalisar Zartarwa ta Kasa. Kuma babu wani Shugaba Mai Cikakken Iko na Najeriya da ya bada dama ga mataimakinsa kamar yadda na yi wa Atiku.

“Ba na bukatar in mayar da shi matsayin Mukaddashin Shugaban Kasa saboda Kundin Tsarin Mulki ya yi bayani filla-filla idan Shugaban Kasa ba ya nan, Mataimakin Shugaban Kasa ya karbi mulki kai tsaye, zai kuma iya tuntuba ne kadai idan ya zama dole.

“Amma tunda ban taba barin kasar nan har na tsawon kwanaki 104 ba a lokaci guda, mutane ba za su sani ba cewa Atiku ya rika wakilta ta duk lokacin da ba na nan”, a kalaman Mista Obasanjo.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan