Kungiyar Kwadago ta yi Allah-wadai da karin kudin fasfo

158
Tutar Kungiyar Kwadago

Shugabannin Kungiyar Kwadago sun yi Allah-wadai tare da sukar yunkurin Gwamnatin Tarayya bisa karin kudin fasfo.

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa, NIS ce ta sanar da cewa daga 4 ga watan Maris za a rika biyan N70,000 ne don samun fasfo din da zai yi shekara goma yana aiki, wanda za a rika yi ta Intanet.

Shugabannin Kungiyar Kwadago sun fada wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN a Lagos ranar Laraba cewa ma’aikata da dama ba za su iya yin tafiya zuwa kasashen ketare ba indai ba a rage kudin fasfon ba.

Mataimakin Sakatare Janar na Kungiyar ULC, Chris Onyeka ya fada wa NAN cewa bai dace a kara kudin samun takardun tafiya ba a lokacin da ‘yan Najeriya ke fama da matsalolin tattalin arziki.

“Gwamnati ta kasa biyan N30,000 ga ma’aikata, amma abu ne mai sauki ta kara kudin fasfo daga N22,000 zuwa N70,000.
“Maganar cewa Hukumar Kula da Shige da Fice ta kara lokacin amfanin fasfo din daga shekara biyar zuwa goma ba dalili ne mai kyau da zai sa a ninka kudin fasfo din ba har sau uku”, in ji Mista Onyeka.

Mista Onyeka ya roki Hukumar Kula da Shige da Ficen ta rage farashin zuwa N40,000 ko N45,000 don ba al’uma damar mallakar fasfon.

“Zai yi wahala ga ‘yan Najeriya su yi tafiya bisa sabon farashin kuma wannan matsalar za ta shafi hakkokinsu na dan Adam”, in ji Mista Onyeka.

Shi ma Shugaban Kungiyar Masu Kamfanonin Sinadarai, Takalma, Roba, Kirgi da Kayan da ba Karafa ba, Olagoke Olatunji ya yi Allah-wadai da sabon farashin, inda ya yi kira da a yi ragi.

Mista Olatunji ya lura da cewa zai dauki ma’aikaci tsawon wata hudu a bisa mafi karancin albashi na N18,000 da ake da shi yanzu kafin ya iya mallakar fasfot din da wannan sabon farashin.

Ita ma a bangarenta, Kungiyar TUC ta ce bai dace Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa ta kara kudin fasfot ba a irin wannan lokaci.

“Kungiyar ta yi Allah-wadai gaba daya da abinda Hukumar Kula da Shige da Fice ta gabatar kuma za mu dauki duk wani mataki da muka ga ya dace don tabbatar da cewa sabon fasfot din na kasa da kasa bai wuce N50,000 ba”, in ji Mista Olatunji.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan