An ceto mutum 89 daga hannun ‘yan garkuwa

147
Haƙƙin mallakar hoto: Hassan Maina Kaina (VOA)

Rundunar Sojin Najeriya ta Operation Sharar Daji ta ce ta ci lagon mahara 21, ta kuma kama ‘yan bindiga 17 tare da ceto mutane 89 da aka yi garkuwa da su a jihohin Katsina da Zamfara.

Rundunar Sojojin Kasa ta bayyana haka ne ranar Talatar da ta gabata ta bakin mai magana da yawunta, Major Clement Abiade.

Major Abiade ya bayyana cewa rundunar ta samu nasarar cafke ‘yan bindigar tare da ceto mutanen a ranakun 22 da 23 ga watan Janairun da ya gabata, inda ta mika su ga iyalinsu.
Rundunar ta ce an yi garkuwa da su ne a kauyen Bukkuyum dake jihar Zamfara.

Bayan haka, Rundunar ta kama wasu mutum biyu masu suna Musa Amadu da Auwal Mutairu da ke kai rahoto ga yan bindiga a kauyen Danfumi da ke garin Birnin Magaji.

Rundunar ta ce an samu asarar rayukan mutum 11 ciki har da wani dan kato da gora guda daya.

Rundunar ta kuma kwace makamai da dama daga hannun maharan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan