Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana wasu muhimman abubuwa uku da zai yi idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.
Mista Atiku ya bayyana haka ne ranar Alhamis da daddare a Abuja yayin wata ganawa da shi da mataimakinsa, Peter Obi wadda Gidauniyar MacArthur ta shirya tare da hadin gwiwar Gidan Talabijin na Kasa, NTA da DARIA Media.
Da yake bada amsar tambayar da aka yi masa akan hanyar da zai bi wajen dakile yan Ta’addan Boko Haram, sai ya ce: “Zan yi bincike akan tsarin sojojin kasar nan domin ba za mu ci gaba da sa ido muna gani sojojinmu na rasa rayukansu tare da makamansu a hannun ‘yan ta’adda ba”.
A bangaren rikicin dake tsakanin manoma da makiyaya, dan takarar ya ce zai wayar da kan makiyaya su koma wuraren ciyar da dabbobi na musamman, domin akwai bukatar yin gangamin wayar da kan al’umma don makiyaya su dinga amfani da wannan hanyar ciyarwa don dakile rikice-rikicen.
Da aka tabo batun cin haci da rashawa, tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce duk wani wanda ya saci kudin gwamnati kuma ya dawo da su, to za a yafe masa laifuffukansa.
A cewarsa, hakan zai ba su damar dawo da kudade da suka sata ba tare da fuskantar hukunci ba.
Ya kara da cewa zai sa tsauraren matakai da za su hana tare da yaki da cin hanci da rashawa.
Daga karshe, ya ce idan ka ce za ka hukunta wadannan mutane, karshe za ka kare ne da hukunta su ba tare da karbo kudaden da suka sata ba.