NDLEA ta yi babban kamu a Akwa Ibom

343
Jami'in Hukumar NDLEA

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa, NDLEA ta jihar Akwa Ibom ta yi babban kamu inda ta kama dilolin kwaya har mutum 120 a karamar hukumar Mbo dake jihar a wani samame da ta gudanar.

Haka kuma Hukumar ta kama katinan zabe guda 244 na mutane dabam-dabam a hannun wani mutum mai suna Okon Bassey.

Mai magana da yawun Hukumar, Muhammad Sokoto ne ya bayyana hakan.

Ya kara da cewa sun samu kilogram 51 na sholisho, da gram 250 na wiwi, da gram 17 na hodar Iblis, da gram 500 na Tramadol, da Diazepam da Polypro.

Sun kuma yi nasarar kama wata babbar dilar wiwi mai suna Joy Adams, kuma tuni suka mika su kotu domin fuskantar hukunci.

Daga karshe, Muhammad Sokoto ya ce kokarinsu na yaki da sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi shi ya taimaka musu wajen bankado miyagun ayyuka na bata gari.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan