Ziyarar Atiku a Amurka: Wani dan jarida Ba’amurke ya tona asiri

164
Atiku da 'yan tawagarsa

Judd Legum, wani dan jarida kuma tsohon Daraktan Bincike na yakin neman zaben Hillary Clinton ya ce Atiku Abubakar ya biya $540,000 don ya samu ya shiga Amurka.

A wani rubutu da ya yi mai taken Me kwangilar kamun kafa ta Dala Miliyan 1.1 za ta siya a Washington din Trump? Legum ya ce yarjejeniyar PDP da Brian Ballard, wani babban mai kamun kafa wanda yake da danganta mai zurfi da gwamnatin Trump ita ta taimaka wa ziyarar ta Atiku.

Kakakin Atiku, Paul Ibe bai dauki kiran da aka yi masa ba, bai kuma bada amsar rubutaccen sako da aka aika masa ta wayarsa ba don ya yi tsokaci game wannan rahoto.

A watan Nuwamba, 2018, jaridar The Cable ta bada rahoto na musamman dake cewa jam’iyyar Atiku, PDP ta sanya hannu bisa wata yarjejeniya da Ballard don inganta dangantakar Amurka da Najeriya wadda za ta mayar da hankali “wajen kiyaye yanayin siyasa da na tsaro ba tare da tsoratarwa ko tsoma baki ba”.

“Zai zama hakkin kamfanin ne ya tuntubi abokin cinikisa ya kuma goyi bayan wasu batutuwa da ya ga sun zama wajibi sun kuma dace a madadinsa a gaban Kotun Gwamnatin Tarayya ta Amurka”, wasu takardun kwangila da jaridar The Cable ta samu suka nuna haka.

“Batutuwa da manufofi za su iya hadawa da inganta dangantakar Amurka da Najeriya, karfafa tare da bunkasa darajojin Dimokuradiyya da kuma doka a Najeriya da mayar da hankali na musamman a watanni masu zuwa wajen kiyaye yanayin siyasa da na tsaro ba tare da tsoratarwa da tsoma baki ba don tabbatar da nasara da adalci a zaben Najeriya na shugaban kasa a 2019”, a cewar takardun.

Atiku, tsohon Mataimakin Shugaban Kasar bai ziyarci Amurka ba tsawon shekaru 12, kuma jam’iyya mai mulki ta rika yi masa ba’a.

Legum ya ce: “Wani tsohon jami’in gwamnatin Amurka ya tabbatar wa da Popular Information cewa an hana Atiku takardar izinin shiga Amurka a hukumance bisa tanadin dokar shugaban kasa da ta ta nufi jami’an kasashen ketare masu tabon cin hanci”.

Ya ce an yi bayanin zarge-zargen cin hanci da ake yi wa Atiku filla-filla a cikin wani rahoton da ya kunshi jam’iyyun siyasa biyu na shekara ta 2010 da Majalisar Dattawan Amurka ta fitar KORAR CIN HANCI NA KASASHEN KETARE DAGA AMURKA: LABARUKAN KUDADE HUDU”.

Ya ce an kuma samu Atiku da hannu a binciken William Jefferson, tsohon dan Majalisar Wakilai ta Amurka wanda ke fuskantar hukuncin zama gidan yarin na shekara 13 sakamakon cin hanci. Koda yake dai dan takarar PDPn ya sha musanta zarge-zargen cin hanci da aka yi masa a rahoton, amma kuma ba a taba gurfanar da shi gaban kotu ba da wani mugun laifi.

Sanarwar Shugaban Kasa 7750
Kafin shekara ta 2018, Atiku ya yi magana a fili game da gazawarsa wajen samun takardar izinin shiga Amurka.

A watan Disamba na shekara ta 2017 ya ce: “Damar Amurka ce ita kadai ta ce ga wanda take so ya shiga kasarsu ko kuwa a’a. Ba gudu nake daga Amurka ba. Na nemi a ba ni, amma ba a ba ni takardar iznin shigar ba”.

Legum ya ce gazawar Atiku shiga Amurka za ta iya kasancewa sakamakon Sanarwar Shugaban Kasa 7750 wadda Shugaba George Bush ya sanya wa hannu wadda ta hana shiga shugabanni masu ci da tsofaffi na kasashen ketare da suke da tabon cin hanci shiga Amurka, musamman wadanda cin hancin nasu yake da danganta a kasar.

“Gwamnatin Amurka ba ta yin bayani a bainar jama’a game da me yasa ake hana daidaikun mutane takardun izinin shiga. Amma wani tsohon jami’in gwamnati wanda ya ga takardun ya tabbatar wa da Popular Information cewa har kwanan nan, an hana Abubakar takardar izinin shiga karkashin Sanarwa 7750”, Legum ya rubuta haka.

Ya ce kwangilar ta bukaci biyan $270,000 nan take da wata $270,000 da za a biya a watan Disamba, 2018.
“Wata daya bayan nan, sai ga Atiku a Amurka, ya kuma dawo Najeriya don yin yakin neman zabe mai karfe don zama shugaban kasa”, Legum ya rubuta haka.

Yanzu Abubakar ya dawo Najeriya, tafiyarsa zuwa Amurka ta karfafa masa gwiwa yayinda yakin neman zabensa ke shiga kwanakinsa na karshe. Taken yakin neman zabensa na Trump ne. Let’s Get Nigeria Working Again” (Mu dawo da Najeriya ta ci gaba da aiki).

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan