Gagarumar Nasarar da Sojojin Najeriya suka yi na Kashe Adamu Rugu-rugu yasa Jama’a Murna

206

Shidai Adamu rugu-rugu sananne ne afadin yankin Gwoza inda yayi kaurin suna a matsayin babbar komandan Boko haram bayan da aka karbi gwoza daga dakarun nigeria a shekara ta 2014.

Bayan nasarar sake kwato garin Adamu rugu rugu yayi sa’ar tserewa daga Gwoza inda ya shiga daji domin samin mafaka.
Sai dai afarkon wannan wata Sojojin najeriya tare da haddin kan Civilian JTF sunyi nasarar kashe Rugu rugu awata samame da suka kai ayankin.

Kamin ya shiga wannan harka ta ta’addancj Adamu rugu rugu ya taba tsayawa takarar kansila inda ya fadi, daga bisani ya cigaba da wa’azin barkwanci kaman yadda ya saba.

Kisan rugu rugu babbar nasara ce domin yana daga Cikin masu jagorantar kai hare-hare a yankin jefi-jefi duk da karya lagon kungiyar da akayi a daukacin yancin,
Al’ummar cikin garin Gwoza sun bazama titi don murnar jin labarin kissar wannan kasurgumin dan ta’adda. Kuma sun yaba da jinjina ga Jami’an tsaro gami da yan sakai na Civilian JTF.
Muna fatan Allah ya Murkushe mana ragowan.
Amin.

Daga
Comr Muhammad Pulka

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan