Gwamnan jihar Kaduna Nasir el-Rufa’i ya ce ba a taɓa ɗan siyasa ko ma’aikacin gwamnati da talakawa suka yarda da shi a kasar nan kamar Shugaba Muhammadu Buhari.
Gwamnan ya ce ‘yan kasar nan sun san tarihin shugaban bai taba cin amana a ayyukan da ya gudanar ba a baya.
Ya ƙara da cewa babu wani dan siyasa a faɗin ƙasar nan da zai iya kayar da shugaba Buhari a fagen siyasa
Ya kuma soki tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo, inda ya ce “idan aka ji Obasanjo na maganganu akwai abin da ya nema a gwamnati bai samu ba. Saboda haka ba don Allah yake yi ba,” in ji Gwamna el-Rufai.
Sai dai ya bayyana cewa har yanzu akwai abubuwan da ya kamata a kara gyarawa a gwamnatin Buhari.
Amma ba zai bayyana su ba, saboda a cewarsa ba ya ba da shawara a kafafen yada labarai. Ya ce idan zai ba shugaban shawara zai kebe ne da shi a fadarsa.
Har ila yau ya bayyana daukar Dokta Hadiza Balarabe a matsayin mataimakiyarsa a zaben 2019 a matsayin wani yunkuri na ci gaban jihar, ba wai don kawo rabuwar kai a bangaren addini ba.
A bangaren korar malamai ya bayyana cewa mafi yawancin malaman da aka korar a jihar “jahilai ne saboda bai kamata a ce suna aji suna koyarwa ba,” in ji ta.