Hukumar EFCC Ta Tabbatar Da Sahihancin Bidiyon Ganduje

82

Hukumar EFCC ta tabbatar da sahihancin bidiyon nan da ya hasko Gwamnan Jihar kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje yana karbar kudi samfurin Dalar Amurka daga hannun ‘yan Kwangila.

Cikin wani rahoto da Jaridar PUNCH ta rawaito ya bayyana cewa Hukumar tayi amfani da ƙwararru masana harkar sadarwa da kafafen yada labarai dake cikin gida da waje, inda suka tabbatar da sahihancin bidiyon.

Tun da farko makusanta gwamnan sun sha musanta sahihancin faya-fayan bidiyon, inda su ke ikirrarin cewa faifan bidiyon kirkirarsa aka yi.

Wannan bincike dai ya kore dukkanin wani zargi da ake yi akan sahihancin faifan bidiyon

Wata majiyar sirri ta bayyana cewa an dakatar da binciken ne domin gudun kada jamiyya mai mulki ta samu matsala a jihar kano.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan