‘Yan sanda sun kashe mutum uku masu garkuwa da mutane a Taraba

125
'Yan Sandan Najeriya

A ranar Lahadi ne jami’an ‘yan sanda na Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Taraba suka kashe mutum uku da ake zargin masu garkuwa da mutane bayan da suka yi musayar wuta da su a yankin Bali dake jihar.

Wata sanarwa da Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Taraban, David Akinremi ya fitar ranar Litinin ta ce wadanda ake zargin ‘yan garkuwa da mutanen ne sun dade suna addabar mazauna yankunan Bali da Suntai dake jihar Taraban.

Mista Akinremi ya ce jami’an ‘yan sandan da suke a ofishin ‘yan sanda na Bali sun yi wa masu garkuwa da mutanen kofar rago ne, suka kuma yi musayar wuta da su.

Ya ce an kashe uku daga cikinsu yayinda sauran suka samu muggan raunuka.

Ya ce an yi musu kofar rago ne yayinda suke yunkurin sace wasu mazauna wani a kauyen Garwa, sun kuma yi garkuwa da iyalin gaba daya.

“Mayar da martani cikin gaggawa da zaratan jami’an ‘yan sandan suka yi tare da tallafin jami’an kato da gora na jihar shi ya haifar da musayar wuta hakan ya haifar da mutuwar uku daga cikin mugayen.

“Wani mamba na ‘yan kato da gora ya samu rauni sakamakon harbin bindiga daga mugayen.

“Abubuwan da aka gano sun hada da bindiga kirar gargajiya mai siffar AK47, albarusai 12, wayoyin hannu guda biyu, kakin soji na bogi, wasu layu da wukake.

“Amma sauran mambobin masu aikata muggan laifukan sun samu raunin harbin bindiga, amma ana ci gaba da shiri na musamman don tabbatar da an cafke su”, in ji Mista Akinremi.

Kwamishinan ‘Yan Sandan ya gargadi masu aikata muggan laifuka a jihar da su sake tunani su kuma daina aikata muggan laifuka.

Ya nanata cewa Rundunar ‘Yan Sandan Jihar a shirye take ta mayar da jihar muhallin da ba zai yi wa mugaye dadin zama ba.

Ya kuma yi kira ga al’umma da su rika bada bayanai masu amfani game da masu aikata muggan laifuka a yankunansu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan