Ganduje ya bada umarnin rufe dukkan filayen wasan jihar Kano gabanin ziyarar Atiku

155
Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje

Gwamnatin jihar Kano ta bada umarnin a rufe manyan filayen wasanni guda biyu dake jihar, kwana shida kafin gangamin yakin neman zaben jam’iyyar PDP.

Jaridar Daily Nigerian ta gano cewa ana sa ran dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar zai yi taron yakin neman zaben nasa ko dai a Filin Wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata ko kuma Filin Wasa na Kano Pillars dake Sabon Gari.

Amma jaridar ta gano cewa Gwamnatin Jihar ta umarci Hukumar Kula da Wasanni ta Jihar Kano da ta rufe filayen wasan don yin kwaskwarima.

Sai dai wata majiya dake da kusanci da Gwamnatin Jihar ta ce an bada umarnin rufe filayen wasan ne don kawo cikas ga yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a jihar.

A cewar majiyar wadda ta nemi a sakaye sunanta, Gwamna Ganduje ya samu rahoton sirri dake cewa ana tattara magoya bayan jam’iyyar PDP a jihar masu yawa don halartar yakin neman.

“Akwai yiwuwar cewa Atiku zai tara mutane fiye da yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya tara lokacin yakin neman zabensa a makon da ya gabata.

“Mutane sun fusata sun kuma gaji da Ganduje.

“Kuma, Gwamnan ba ya so ya aika da mummunar alama zuwa Abuja saboda taron mutanen zai zama ba masaka tsinke”, a cewar majiyar.

Lokacin da aka tuntubi Abbati Sabo, mai magana da yawun Hukumar Kula da Wasanni ta Jihar Kano, ya ce ba an bada umarnin ne don a kawo cikas ga taron yakin neman zabe na dan takarar jam’iyyar PDPn ba.

Ya ce an bada umarnin yin kwaskwarimar ne gabanin kakar wasannin Nigeria Premier Leage, NPL.

Ya ce an shawarci Gwamnatin Jihar da ta yi kwaskwarimar saboda tuni kakar wasannin ta fara.

“A iya sanina, wannan umarnin ba shi da danganta da siyasa. An ba Gwamnatin Jihar shawarar ta bada umarni a gyara filayen wasan kafin kakar wasanni ta NPL.

“A yanzu Gwamnatin ta karbi wannan shawara ta kuma bada umarnin fara fara aikin don fara kakar wasannin cikin nasara. Kamar yadda za ka iya gani, filayen wasan suna bukatar gyara, yanzu kuma Gwamnatin ta amsa kiran a yi kwaskwarimar”, a kalaman Mista Sabo.

An gano cewa za a fara kwaskwarimar ne daga 4 ga watan Fabrairu zuwa 18 ga watan na Fabrairu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan