Ku san irin ‘yan takarar da za ku zaba- Shawarar Okorocha ga Ibo

39
Gwamna Rochas Okorocha na Jihar Imo

Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo ya shawarci ‘yan kabilar Ibo da su lura sosai a yayin zaben 2019.

Mista Okorocha, wanda ya yi gargadin yayin wani taron manema labarai ranar Talata a Gidan Gwamnati dake Owerri ya bayyana siyasar da ake ciki a matsayin wani ‘yaki mai sabon salo’.

Ya ce Ibo za su yi da-na-sani sosai idan ba su lura ba wajen zabe, yana mai lura da cewa zaben da suka yi a baya bai tsinana musu komai ba.
Yayinda yake kira da a zabi jam’iyyar APC, Gwamnan ya yi kira ga Ibo da kada su lura da dan abinda za a ba su nan take, ya yi kira a gare su da su yi duba zuwa gaba.

Ya ce zaben wani dan takara ba Shugaba Buhari ba zai sa a ci gaba da yi wa Ibo mulkin mallaka, abinda ya lashi takobin yaka.

“Akwai sabuwar gwagwarmayar siyasa a Najeriya wadda ta yi kama da yakin basasa lokacin da Ibo suke tafi yaki ba tare da sanin abinda suke shiga ba.

“Irin wannan yakin yana zuwa amma a wani salo na daban, kuma yana bukatar hikima, idan a’lumar Ibo ba su yi halin kwarai ba a wannan lokaci, za su wahala a siyasance”, in ji Okorocha.

Gwamnan ya yi bayanin cewa bukatarsa ta zama sanata shi ne don ya kare muradun a’lumar Imo musamman da kuma Ibo gaba daya, don kuma a ci gaba da damawa da shi a siyasance.

Ya ce abin haushi ne yadda wasu ‘yan Majalisar Dokoki dake wakiltar yankin suke azurta kansu kawai, abinda ya yi alkawarin canzawa idan aka zabe shi.

Turawa Abokai

1 Sako

  1. Do you have any kind of pointers for composing write-ups?

    That’s where I always battle as well as I simply wind up gazing vacant screen for long period
    of time.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan