Siyasar Daba ga Matasa ko Gudu a Duhu (1)

176

Siyasa ta ginu ne ta fannin Dumukuradiyya kowa yana da yanci ya shiga jam’iyyar da yaga ta kwanta masa a zuciyarsa, ko kuma ya fada jam’iyyar da uban gidansa yake ciki. Haka yasa ko wacce jam’iyyar siyasa take rike kan madafan ikon domin kawo sauyi mai kyau na cigaban al’umma. Wannan yasa muka aro tsarin mulkin kasar America, duk da mun sha ban-ban dasu wajan tsarin mulki, amma dai siyasar iri daya ce.

A kasar Nigeria akwai majalisun kasa guda biyu, majalisar wakilai da majalisar dattawa wanda a kasar America majalisa daya suke da ita kawai ta wannan fannin muka sami banbanci daga kasar da muke kallo ta fannin mulki da siyasa.

Haka a siyasa shi ma mun dan sha ban-ban da kasar American kadan, mu muna da jam’iyyun siyasa sama da hamsin, su kuma suna da jam’iyya biyu kawai. Sai dai a iya bancike na banga inda wani jagoran siyasa ya fita daga wata jam’iyya ya fada wata jam’iyya ba, saboda gudun tsira.

Shugabannin Nigeria suna neman mulki ne domin gina kansu, ba kasar su ba ko al’ummarsu. Bazan ce sun gaji wannan bane daga kasar da suka yi mana mulkin mallaka a shekarun da suka shude. Saboda wannan tarihi in nace zan bude shi to abu ne mai fadin gaske, amma dai zamu sami lokaci mukalli mulkin mallaka ta fannin ilimi da siyasa.

A duniya babu inda ake siyasar sara suka da bawa matasa kwaya kamar Nigeria wannan kasa tayi shura wajan siyasar daukar makami tun a jamhuriya ta farko matsalar kuma taci gaba da bibiyar mu har jamhuriyya ta hudu wadda muke ciki yanzu. Wannan dalili ya kawo koma baya na siyasa da matasa.

Matasa sune kashin bayan siyasa a kowace al’umma a tarihin duniya; amman matasan Nigeria sun sha ban-ban wajen irin rawar da suke takawa a siyasar Nigeria a dalilin daba da ta’ammali da kayan maye da suke yi.

Daba kalma ce da take bayyana wata iriyar halayya ta matasa, wadda take haifar da sakamako mummuna. Daba ta na bada hoto na gungun matasa, masu shan kayan maye (kamar giya, ko ganyen wi-wi, ko kwaya, ko roti, ko Benalin, da makamantan su), masu daukar makami, suna farma wadanda ba su ji ba ba su gani ba, ko kuma su farwa junansu, ko su farwa wanda aka saka su farwa.

Matasa suna gudu a duhu na rashin sanin ina suka dosa, na harkar siyasa ko bangar siyasa, jagaliya da makamantansu.

Duk mai ilimi yana sane da cewa daga anyi zabe siyasa ta kare, kuma sai bayan wa’adin mulkin ya kare za’a dawo siyasa. Amma anan Nigeria ba haka abin yake ba. Daga lokacin da aka gama siyasa, matasa suna zama mabarata a offishin yan siyasa da gadin offishin iyayen gidansu,fadanci, banbadanci da sara suka.

Daga
Shuaibu Lawan,
shuaibu37@gmail.com
08037340560 Saƙo kawai (Text Only)

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan